Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

  • Gwamnan jihar Katsina ya bayyana dalilansa na cewa, ba a taba yin shugaba kamar Buhari ba a Najeriya
  • A cewarsa, a mulkin shugaba Buhari ne kadai talaka ke morar abinda ya fito daga hannun gwamnati
  • Ya kuma yaba wa shugaban kasa bisa kirkirar shiri wanda talaka zai san ana mulki sabanin gwamnatocin baya

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana gwamnatin APC a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi kyawun gwamnatin da Najeriya ta taba yi tun bayan ayyana kasar a shekarar 1914 da Turawan mulkin mallaka suka yi.

Ya gargadi sassan Najeriya game da abinda ya bayyana a matsayin rashin adalci kan gwamnatin Shugaba Buhari, yana mai cewa ya kamata 'yan Najeriya su yaba duba da matsalar tattalin arziki da gwamnatin ke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta a 2015.

Ya ta'allaka matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

KARANTA WANNAN: Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

Ba a taba yin shugaba na-gari kamar Buhari ba tun kafa Najeriya, Masari ya bayyana dalili
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: encomium.ng
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da masu ruwa da tsaki don kidaya masu cin gajiyar shirin ciyar da 'yan makaranta na kasa na jihar, ya kuma ce dole ne mutane su yaba da cewa a cikin wannan lokacin sun ji kasancewar gwamnati da tasirinta a rayuwar talakawa .

Ya kawo misali da aikin ciyar da makarantu, tare da wasu tsare-tsaren gwamnati na damawa da jama’a wanda aka kashe biliyoyin nairori don talakawa a cikin al’umma.

Da yake yabawa shugaban, Masari ya ce:

“Ko ka so Buhari ko ba ka so, ya sake fasalta yadda ake gudanar da mulki ta yadda talaka wanda bai taba sanin meye gwamnati ba yanzu yana jin tasirin gwamnati.

Gwamnan ya nace cewa, babu wata gwamnatin da taba yi a Najeriya talaka ya mora ya kuma san ana yi dashi kamar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a ra'ayinsa shine dalilin da yasa ba a taba samun mulki kamar nasa ba.

Kara karanta wannan

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

Yayin da ake koka wa kan matsanancin halin tattalin arziki, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce Najeriya ba za ta bukaci bashi daga waje ba idan aka dawo da kudaden da gurbatattun 'yan siyasa da shugabannin kasa suka sata suka kai bankunan kasashen waje.

Kakakin hukumar, Azuka Ogugua, ne ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli a Abuja yayin da take magana a ranar Tarayyar Afirka ta Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ake yi kowacce ranar 11 ga watan Yuli, jaridar The Punch ta ruwaito.

Jaridar ta yi ikirarin cewa gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta na fama da kudade kuma ta ci bashin N20.8tn tun lokacin da ta hau karagar mulki a watan Mayun 2015, inda ya kawo bayanai daga Ofishin Kula da Bashi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

KARANTA WANNAN: Gwamnan Gombe ya bayyana matakan da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

A wani labarin, Aiki a bankunan kasuwanci a Najeriya ya kasance aiki mai matukar cike takaici, kamar yadda wani matashi mai suna Basit ya koka kan yanayin aikin da yake a banki.

Matashin mai shekaru 28, wanda aka sakaya sunansa don kare bayanansa, yana aiki a matsayin jami'in bayar da kudi a bankin Fidelity a Najeriya tun shekarar 2015.

Shekaru shida, yana reshen Fidelity, yana aiki a matsayin da aka dauke shi, da karamin albashin Naira 68,000 ($ 165) a wata ba tare da karin girma ba. Ba ka'ida ne aikin Basit ya rasa ba, tsarin da yake aiki a karkashinsa ne matsalar. A rubuce shi ba cikakken ma'aikaci bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.