'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari wajen fasa duwatsu, sun hallaka wani mutumin sun sace wani
  • Rahoto ya bayyana cewa, tuni an binne wanda aka kashe, yayin da ake jiran kira kan batun wanda aka sace
  • Rundunar 'yan sanda bata tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ta ce tana kan bincike a kai

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari a wani wurin fasa duwatsu a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, inda suka kashe wani ma’aikaci a wurin, Ibrahim Aliyu, tare da yin awon gaba da wani, Abdul Umar Ekuji.

Wani mazaunin yankin, mai suna Salihu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:43 na yamma a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK47 sun mamaye wurin da ake fasa duwatsun, wanda ya ce yana da nisan kilomita biyu da bainar jama’a.

KARANTA WANNAN: Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikaci, Sun Yi Awon Gaba da Wasu
'Yan bindiga | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Twitter

Aliyu, wanda ke aikin fasa dutse, ya tafi gida amma aka sanar dashi game da mamayar da 'yan bindigan suka yi wa yankin.

Salihu ya ce:

"Dawowarsa kenan daga wurin ba a fi minti 20 ba lokacin da aka sanar dashi cewa masu satar mutane sun mamaye wurin da ake fasa duwatsun."
“Ya dauki wasu 'yan banga biyu a kan babur dinsa don ya tunkare su. A kan hanyarsa ne, wani dan bindiga ya harbeshi a kirji nan take ya mutu."

Ya ce wasu ma'aikatan wurin fasa dutsen sun tsere da kyar, amma wani mai suna Abdul Umar Ekuji, 'yan bindigan sun yi awon gaba dashi.

Salihu ya ce an binne gawar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, duk da cewa ya ce har yanzu iyalan wanda aka sace din basu ba da rahoton an tuntube su ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani game da lamarin ba, amma ya ce zai tuntubi DPO mai kula da yankin a karamar hukumar Toto.

'Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun wawashe shagon cajin wayoyi

Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu hudu suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Danmusa, karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan sanda sun kawo agajin gaggawa kuma sun dakile harin wanda ya dauki kimanin minti 40, yayin da maharan suka wawushe wani kantin cajin wayar salula.

Majiyar ta ce maharan sun zo ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Asabar suka fara harbin kan mai uwa da wabi a garin, inda suka kashe mutum daya kuma suka ji wa daya rauni, ta kara da cewa an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

KARANTA WANNAN: Annobar Korona: An Garkame Wasu Makarantu Biyu Saboda Tsoron Ta'azzarar Korona

An Cafke Wasu 'Yan Bindiga Bayan Karbar Kudin Fansa Da Kashe Wanda Suka Sace

A wani labarin, Jami’an ‘yan sanda a jihar Abia sun cafke gungun 'yan bindiga, wadanda suka kware a harkar satar mutane tare da neman kudin fansa, Channels Tv ta ruwaito.

Fiye da mutane takwas da ake zargi jami’an tsaro na jihar suka cafke, an ce biyu daga cikinsu sun kashe wanda suka sace bayan sun karbi kudin fansa na naira dubu dari bakwai (N700,000).

An kuma ce sun sayar da mota kirar Lexus ta mutumin da suka kashen a kan kudi naira dubu dari biyu (N200,000).

A yayin zantawa da manema labarai a Umuahia, Kwamishinar 'yan sanda, Janet Agbede ta ce tsagerun sun kasance cikin binciken 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar a cikin 'yan kwanakin nan bisa aiwatar da fashi da makami da ayyukan satar mutane a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel