Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga
- Rahoton da muke samu ya shaida cewa, jami'an tsaro da dama sun tsunduma daji domin neman Sarkin Kajuru
- Rahoton ya ce, hadakar jami'an 'yan sanda dana sojoji sun fara aikin ceton bayan da suka samu labarin sace Sarkin
- An sace Sarkin Kajuru a karshen mako, inda aka tattara shi da wasu iyalansa sama da goma
Sojoji sun mamaye dajin Kaduna don neman Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu da wasu danginsa 10 da aka yi garkuwa da su a karshen mako, The Nation ta ruwaito.
Satar sarki ya biyo bayan sace wasu dalibai da aka yi a wata makaranta duk dai a jihar ta Kaduna, lamarin da ya sake jefa al'umma cikin tsoro. Jami'an tsaro na aiki don ganin an ceto su.
Baya ga sojojin da ke gandun daji, rundunar 'yan sanda ta ce suna sa ran rundunar dabaru ta Babban Sufeto-Janar na 'Yan Sanda zata ba su goyon baya ta fasaha.
KARANTA WANNAN: Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah
A wata sanarwa daga kakakin rundunar ta jihar Kaduna a ranar 11 ga watan Yuli, Muhammed Jalige, ya ce:
“Rundunar 'yan sanda ta Kaduna ta bakin jami’in ‘yan sanda na shiyya (DPO) na Kajuru dake Kaduna ta sami wani rahoto mara dadi game da sace Sarkin Kajuru, Mai martaba, Alhaji Alhassan Adamu a safiyar yau, 11 ga Yuli 2021.
Da yake tabbatar da jami'an tsaro na aiki don ganin an ceto Sarkin da iyalansa, Jalige ya ce:
”Amma duk da haka, hadin gwiwar sintiri na rundunar 'yan sanda ta ‘yan sanda (PMF), da 'yan sanda na yau da kullum, da kuma Sojojin Najeriya da ke aiki a karamar hukumar Kajuru a yanzu haka suna aikin bincike da ceto a dajin don samun damar kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da aka tuntubi rundunar ta IGP don ba da tallafi na fasaha.”
Yadda 'yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13
'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru tare da 13 daga cikin iyalansa a wani samamen cikin dare da suka kai, Sahelian Times ta ruwaito.
Alhaji Alhassan Adamu tsohon basarake ne mai shekaru 85 mai daraja ta biyu an yi awon gaba dashi tare da matansa uku, jikokinsa biyu, hadimansa uku da wasu mutum biyar.
Daya daga cikin manyan masarautar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da aukuwar harin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin jikokin basaraken mai suna Saidu Musa mai rike da sarautar Dan Kajuru ya tabbatar da aukuwar lamarin.
KARANTA WANNAN: Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi
Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna
A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun sace mutane shida ciki har da yara a garin Milgoma da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a yayin da 'yan bindigan suka zo da yawa suka afka wa jama'a.
Wani dan acaba da aka kaiwa harin, yanzu haka yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.
Asali: Legit.ng