Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello

Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello

  • Kungiyar matasan Arewa ta shawarci kungiyar Ohanaeze da ta kyale tsarin dimokiradiyya ya taka rawa wajen zaben wanda zai gaji Shugaba Buhari a 2023
  • AYCF ta ba da wannan shawarar ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, yayin da take martani kan maganar da Ohanaeze ta yi kan Gwamna Yahaya Bello
  • Bello, wanda aka yi amannar cewa yana hararar kujerar Shugaban kasa a 2023, ya ce ba a rubuta mulkin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ba

Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYFC) ta caccaki kungiyar Ohaneaze saboda ta amince da "tsarin da ake kira mulkin karba-karba" gabanin babban zaben 2023.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma Legit.ng ta gani, ta lura cewa babu inda za a iya samun tsarin mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahra Buhari

Kara karanta wannan

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari

Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello
Kungiyar Arewa ta caccaki Ohanaeze kan furucinta game da Yahaya Bello Hoto: Yerima Shettima.
Asali: UGC

Dangane da kin amincewa da matsayin Gwamna Yahaya Bello kan shugabancin karba-karba da Ohaneaze ta yi, AYCF ta bayyana takamar kungiyar a matsayin mara amfani.

AYCF, ta bakin shugabanta na kasa, Yerima Shettima, ta bukaci masu ruwa da tsaki na kasar da su tsaya kan “cancantar” duk wani dan takarar shugaban kasa sabanin kabilanci-yanki ko addini.

Sanarwar ta ce, shugabannin Arewa da matasan yankin sun yi nisa sosai, sannan ta kara da cewa wani ba zai iya tsoratar da su ba ko kuma a tursasu goyon bayan dan takarar wani yanki ba a zaben Shugaban kasar na 2023.

Kungiyar ta bayyana ikirarin da Ohanaeze ta yi na cewa Gwamna Bello dalibi ne lokacin da ‘yan Najeriya irin su marigayi Dr. Abubakar Rimi, Solomon Lar da sauransu suka ba da shawarar cewa ya kamata ayi karba-karba a matsayin abun dariya.

KU KARANTA KUMA: Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Ƴan Boko Haram a Borno

Kara karanta wannan

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

AYCF ta ce:

"Shin ba abin kunya ba ne cewa Ohaneaze tana bin shawarar da aka bayar shekaru 23 wanda bai da goyon bayan wata doka da aka sani a siyasa yayin da take tuhumar kyakkyawar shawarar da matashin gwamnan ya bayar game da bin cikakken tsarin dimokiradiyya
"Korafin Ohanaeze cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ma ya ci moriyar shugabancin kasar saboda tsarin karba-karba, AYCF ta ce wannan bai isa hujja ba saboda ba ma lokacin yankin kudu maso kudu bane na samar da Shugaban kasa a wancan lokacin."

Dangane da jaddadawar Ohaneaze cewa "ɗabi'a" tana gaba da kundin tsarin mulki, AYCF ta ce ƙungiyar Ndigbo ta yi ƙazamar riba, tana mai cewa babu inda a tsarin dimokiradiyya aka ce ɗabi'a yana gaban kundin tsarin mulki.

AYCF ta kuma mayar da martani ga ikirarin Ohanaeze cewa taron da aka yi kwanan nan na Kungiyar Gwamnonin Kudu ya amince da mika mulki ga kudu a shekarar 2023, tana mai cewa hakan bai ba Ohanaeze lasisin yin watsi da matakai masu sauki na dimokiradiyya ba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Tsohon gwamnan Zamfara ya yi watsi da shawarar gwamnonin kudu, ya ce zai yi takara a 2023

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ahmed Sani Yerima, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 duk da matsayar da kungiyar gwamnonin kudu suka dauka a baya-bayan nan.

Kungiyar a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, ta nace cewa ya kamata a mika shugabancin kasar ga yankin Kudancin Najeriya a 2023.

Yayin da yake magana a Abuja tare da wasu ‘yan jarida, Sanata Sani ya ce ba zai yi watsi da kudirinsa ba tunda babu wani tanadi na mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma kudin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng