Abu Kamar Wasa: Yadda Yara 10 Suka Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa

Abu Kamar Wasa: Yadda Yara 10 Suka Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa

  • Wasu iyalai 10 sun mutu bayan cin tuwon daya, lamarin da ya girgiza shugaban iyalan
  • Ya shaidawa manema labarai cewa, lamarin ya zo masa ne kamar wasan kwaikwayo
  • Ya kuma bayyana cewa, shi da sauran iyalansa shida ne suka tsira daga wannan bala'i

Wani mahaifin yara 10 da suka mutu bayan sun ci tuwon dawa a kauyen Jangeme, Malam Musa Mai icce, ya ce shi da sauran iyalansa shida ba su ci abincin ba saboda ba sa gida.

Mai icce wanda ya yi magana da jaridar Punch a ranar Asabar ya ce babbar diyarsa ce ta dafa abincin da rana kuma iyalansa 10 suka ci.

"Ni kaina, Rafiatu, Bashar, Babangida, Rabi da Suwaiba ba ma gida."

Ya lura cewa dukkan iyalan nasa da sun mutu da kowa yana gida kuma ya ci abincin.

KARANTA WANNAN: Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

Abu Kamar Wasa: Yadda Yara 10 Sun Bakunci Lahira Daga Cin Tuwon Dawa
Taswirar Jihar Zamfara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mai icce ya ce:

“Yarinyata ce ta dafa abincin, (tuwon dawa) da rana kuma yara 10 da ke gida suka ci shi yayin da mu shida ba mu nan.
"Wani makwabcina ya kira ni a waya cewa daya daga cikin yara na yana gudawa da amai. Da sauri na dawo gida na kai shi asibiti.
"Lokacin da nake asibiti, an sake kirana cewa sauran yaran sun kamu da gudawa da amai. Na dawo gida na kai su asibiti inda uku daga cikinsu suka mutu da daddare, sauran bakwai kuma suka mutu washegari.

Ya ci gaba da cewa abin da ya faru kamar wasan kwaikwayo ne a gare shi, yana mai jaddada cewa bai taba shiga irin fitinar da ya shiga ba.

A cewarsa:

“Na yi matukar girgiza sakamakon bala'in amma na bar wa Allah komai a matsayina na Musulmi.
"Ya kasance kamar wasan kwaikwayo a gare ni. Na san ta haka ne aka kaddara ajalinsu. Mu da ba mu gida a wannan rana ba a kaddara mana mutuwa a lokacin ba. Idan ba haka ba, da mun kasance a gida muma mun ci abincin mun mutu."

Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan kwankwaɗar wani maganin gargajiya

Mutane 10 yan gida daya a garin Gwanara a karamar hukumar Baruteen na jihar Kwara sun riga mu gidan gaskiya bayan sun sha wani maganin gargajiya a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Abin bakin cikin ya jefa mutanen garin na Baruteen da mafi yawancinsu Fulani ne cikin dimuwa da damuwa.

Ba a samu cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru ba a lokacin hada wannan rahoton.

Wasu yan garin da aka yi magana da su a wayan tarho sun ce garin na da nisa sosai daga babban birnin jihar, Leadership ta ruwaito.

A cewarsu, fulanin da abin ya faru da su ba masu yawo bane, asalinsu yan garin Kaiama ne.

KARANTA WANNAN: Bayan Kame Nnamdi Kanu, Sojin Sama Sun Yi Kaca-Kaca da Sansanin IPOB

Najeriya Ta Hada Kai da Majalisar Dinkin Duniya Don Samarwa Kasa Abinci Mai Kyau

A wani labarin daban, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo na jagorantar hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dinkin Duniya don inganta tsarin abinci a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na nufin magance yunwa, magance rashin abinci mai gina jiki, rage cututtukan da ke da alaka da abinci da sauransu.

Osinbajo, a cikin jawabin da ya gabatar a taron tattaunawa na hadin gwiwa a Abuja, ya ce kokarin samar da tsarin abinci mai dorewa ya yi daidai da tsarin gwamnatin Buhari na kawar da talauci a duk fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel