Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023

Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023

  • Kungiyoyin Arewa sun bayyana matsayar su game da dokar hana kiwo a fili na gwamnonin kudu
  • Kungiyoyin hadin gwiwa na makiyayan arewa sun ce shawarar ba ta zo da mafita ga masu kiwon shanu
  • Bugu da kari, kungiyoyin sun yi hasashen cewa matsayar za ta yi aiki a kan kudu yayin zaben shugaban kasa na 2023

Shawarar da gwamnonin kudu suka yanke na hana kiwo a fili a yankin bai samu karbuwa ba sosai daga wasu kungiyoyin arewa.

Harma, kungiyar cigaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) ta ce matsayin gwamnonin zai zo da wasu munanan kalubale da zasu haifar a kasar.

KU KARANTA KUMA: 2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba

Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023
Kungiyoyin Arewa sun ce hana kiwo a fili ba abu ne mai yiwuwa ba Hoto: Governor Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Alhaji Ibrahim Abdullahi, sakataren kungiyar GAFDAN na kasa, ya fadawa jaridar Nigerian Tribune cewa haramcin zai kawo cikas ga yankin musamman a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba

Abdullahi ya bayyana cewa da wannan shawarar, kudu tana fatattakar ‘yan arewa masu jefa kuri’u daga yankin.

Da yake ci gaba da magana, ya nuna cewa ba daidai ba ne kuma abin takaici ne ga gwamnan ya kawo karshen tsarin samar da riba ga makiyaya ba tare da samar musu da wata mafita ba.

Kalamansa:

“Mutum baya buga siyasa kawai. Wasu mutane na so mulki ya koma yankinsu kuma suna ganin cewa hanya daya tilo da za'a bi ita ce tsoratar da wasu. Kuna son mulki ya dawo Kudu kuma kuna korar mutane, kimanin masu jefa kuri'a miliyan 17 (Fulani). Babu shakka wannan matakin zai kawo cikas ga damar da Kudu ke da shi na samar da shugaban kasa na gaba a shekarar 2023. ”
“Matsayar kungiyar abin takaici ne matuka saboda ba ka dakatar da wani tsarin sai dai idan ka samar da wani madadinsa. Ba mu adawa da duk wata sabuwar hanyar kiwon dabbobi saboda mun yi imanin cewa tsarin yanzu ya tsufa amma kuma ba za ku hana shi dare daya ba ba tare da samar da wani mafita ba. Don haka, matsayin gwamnonin abu ne da ba zai yiwuwa ba a karkashin tsarin da ake da shi yanzu a Najeriya."

Kara karanta wannan

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

KU KARANTA KUMA: An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas

Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce ba zai yi kasa a guiwa ba wurin ba kowanne bafulatani fili in har yayi niyyar kiwon shanunsa amma a killace.

A yayin jawabi a Abuja a bikin cikar Farfesa Iyorwuese Hagher shekaru 72 a duniya, Ortom ya musanta ikirarin da ake na cewa yana fada da Fulani, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce tarihi ya nuna cewa jama'ar jihar na da alaka mai kyau da Fulani. Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta soki dokar hana kiwo a fili ba inda tace kiwo a killace yafi komai amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel