2023: Obasanjo zai kirkiri sabuwar jam'iyya, ya zabi gwamnoni uku su jagoranceta

2023: Obasanjo zai kirkiri sabuwar jam'iyya, ya zabi gwamnoni uku su jagoranceta

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa, ya shirya tsaf don kafa sabuwar jam'iyya
  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar har ya fara shirye-shirye
  • Tuni an ce ya zabi wasu jiga-jigan siyasar da yake son su jagoranci tafiyar da jam'iyyar

Rahotanni da Legit.ng Hausa ke samu sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo na aiki kan kirkirar wata sabuwar jam'iyyar da za ta dauki mambobin jam'iyyar adawa ta PDP da mai ci ta APC wadanda ke cikin damuwa gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Wata majiya mai karfi ta fadawa jaridar Vanguard cewa Obasanjo ya gamsu cewa akwai yiwuwar manyan jam'iyyun siyasar biyu su shiga cikin rikice-rikice na doka da siyasa wanda zai bar su cikin mummunan hali, watakila ya kai su rasa jagorancin kasar a zaben na 2023.

Majiyar ta ce duk da cewa tsohon Shugaban kasar ya yayyaga katin zama dan jam’iyyar PDP tare da yin murabus daga siyasa, amma har yanzu yana himmatuwa wajen hada kan ’yan Najeriya don yin tasiri kan fitowar shugaban kasa na gaba, gwamnoni da sauran shugabanni.

KARANTA WANNAN: Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara

Obasanjo zai kirkiri sabuwar jam'iyya, ya zabi gwamnoni uku su jagoranci aikin
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Game da sabuwar jam'iyyar, majiyar ta ce:

“Duk da cewa ba a bayyana sunan wannan jam’iyya ba a yayin da muke magana, Baba yana matukar tattara magoya bayansa da kuma masoyansa a duk fadin kasar nan domin ya cika burinsa na kafa gwamnatin da za ta amsa masa."

A cewar majiyar Obasanjo yana fatan dawo da manyan membobin manyan jam'iyyun siyasar biyu zuwa sabuwar jam'iyyarsa sakamakon shirye-shiryen da ke tafe na 2023, in ji SaharaReporters.

Don karfafa samun nasarorin kafa jam'iyyar, Obasanjo ya samu wajen hada sabuwar jam'iyyar, an tattaro cewa ya shirya ganawa ta musamman tare da masoyansa da abokansa a ranar Talata, 13 ga watan Yuli.

Ana sa ran za a bayyana tsaffin gwamnoni uku na jihohin Osun, Jigawa da Kwara da sauran jiga-jigan siyasa da suka fito daga shiyyoyi shida na kasar nan, da kuma tsarin tafiyar siyasa zai bayyana nan kusa.

Majiyar ta kara da cewa:

"Tsoffin gwamnonin uku za su hada karfi da karfe wajen tsara ayyukan jam'iyyar a shiyyar Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Kudu Maso Yamma yayin da ake kokarin kara sanya sunayen wasu masu kula da sauran yankunan kasar."

KARANTA WANNAN: 'Yar Shugaba Buhari Ta Ciri Tuta, Ta Yi Digirgir a Daukar Hoto a Kasar Waje

Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

A wani labarin daban, Tun bayan da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya koma jam'iyyar APC, shugaban riko na jam'iyyar Maimala Buni ya sanar da nadin gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Bayyana Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC ya jawo fushi ga wasu jiga-jigan 'yan siyasar jihar Zamfara, wadanda suka hada da, tsohon gwamna Abdulaziz Yari da tsohon dan majalisar dattawa Kabiru Marafa yayin da suka ki amincewa da nadin.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Yariman Bakura, ya bayyana amincewarsa da nadin, tare da bayyana dalilai daga tsarin mulkin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel