Shugaban kasa a 2023: Tana shirin karewa Atiku, Kwankwaso, Tambuwal da sauransu
- Dukkanin gwamnonin kudu maso kudu 17 sun hade kan batun shugabancin 2023 a bisa ga sabuwar sanarwar da suka fitar
- Da wannan hadin kan, wasu ‘yan siyasan arewa masu sha'awar mukamin zasu jira wani lokacin don cimma burinsu
- Wasu daga cikin ‘yan siyasar arewa da suka nuna sha'awar su sun hada da Atiku Abubakar, Sani Yerima
Gwamnonin jihohin kudu 17 sun dage kan cewa dole ne shugaban kasar na gaba ya fito daga yankin. Wannan shawarar (idan har ta kai ga cimma nasara) zai kawo karshen burin wasu manyan 'yan siyasa daga arewa wadanda ake ganin suna hararar kujerar shugaban kasa a 2023, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnonin sun gabatar a cikin wata sanarwa cewa:
"Kungiyar ta sake jaddada kudirinta na siyasa bisa daidaito, adalci sannan kuma ta amince baki daya cewa shugabancin Najeriya ya kasance tsakanin kudu da arewacin Najeriya kuma sun yanke shawara cewa shugaban Najeriya na gaba ya fito daga yankin kudu."
KU KARANTA KUMA: Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina
Ga jerin wasu manyan ‘yan siyasa a Arewa da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023. Suna nuna sha'awar su kai tsaye ko ta wakili.
1. Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
2. Tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso
3. Gwamnan Yahaya Yahaya
4. Gwamna Aminu Tambuwal
5. Gwamna Bala Mohammed
6. Tsohon gwamna Ahmed Sani Yarima.
KU KARANTA KUMA: An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti
Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu
A wani labarin, Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.
Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.
Asali: Legit.ng