Bayan Shan Kashi a Osun, Shugaban Matasan APC Ya ba Jam'iyyar Mafita kan Zaben 2027

Bayan Shan Kashi a Osun, Shugaban Matasan APC Ya ba Jam'iyyar Mafita kan Zaben 2027

  • Dayo Israel ya ce APC ta daina dora laifin shan kaye a zabe Osun kan wasu mutane, ta yi wa kanta bincike domin gano abin da ya jawo rashin nasara
  • Shugaban matasan na APC ya ce sakamakon zaben Osun ya zama gargadi ga jam’iyyar gabanin babban zaben 2027
  • Israel ya ce farin jinin Ademola Adeleke a tsakanin talakawa bai kamata a raina shi ba saboda rawa da waka da yake yi a bainar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dayo Israel, ya ce dole jam’iyyar ta fuskanci dalilan da suka jawo kayenta a zaben gwamnan jihar Osun maimakon dora laifi ko bayar da uzurin bayan zabe.

Israel ya ce sakamakon zaben ya kamata ya zama babban gargadi ga jam’iyyar mai mulki gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: 'Yan takarar gwamna 2 sun janye, sun mara wa Adeleke baya

Dayo Israel ya gano kura-kuran APC
Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel Hoto: @dayoisrael
Source: Twitter

Dayo Israel ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026.

APC ba ta ji dadin sakamakon zaben ba

Israel ya amince cewa sakamakon zaben ya bata wa ‘yan APC rai, amma ya ce dole jam’iyyar ta mutunta hukuncin masu kada kuri’a tare da yin gaskiyar bincike kan abin da ya faru.

Ya taya Adeleke da al’ummar jihar Osun murnar nasarar, sannan ya yaba wa Oyebamiji, mambobin APC, wakilan jam’iyyar da masu aikin sa-kai da suka shiga takarar.

“Taya murna bai kamata ya maye gurbin yin nazari kan abin da ya faru ba,” in ji shi, yana gargadin cewa jam’iyyar ba za ta iya shiga zaben 2027 ba tare da ta dauki darussan da ta koya daga Osun ba.

A cewarsa, bai kamata a takaita sakamakon zaben da dabarun yakin neman zabe ko ayyukan wasu ‘yan siyasa kadai ba, sai dai a duba shi ta fuskar alakar jam’iyyar da masu kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Makinde: 'Dan takarar shugaban kasa ya samo mafita ga 'yan adawa gabanin 2027

Darasin Tinubu daga zaben Osun

Israel ya ambaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Adeleke cikin mutanen da matsayinsu da salon siyasar da suka bi suka bayar da muhimman darussa daga zaben.

Ya yaba wa Tinubu saboda barin al’ummar Osun su yi amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a ba tare da Fadar Shugaban Kasa ta yi amfani da karfinta wajen karkatar da sakamakon zuwa ga APC ba.

Shugaban matasan na APC ya ce Shugaban kasar na da hanyoyi da dama da zai iya amfani da su, amma ya zabi kada ya yi amfani da ikon gwamnatin tarayya ta hanyar da za ta iya rage wa zaben sahihanci.

“Wata kila Shugaba Tinubu ya rasa Osun ga APC, amma ya samu wani abu mafi girma ga Najeriya: wata dama ta nuna cewa kuri’ar al’ummar Najeriya dole ta kasance da muhimmanci,” in ji Israel.

APC ta sake kallon Adeleke

Ya kuma bukaci ‘yan APC su sake duba yadda suke kallon Adeleke, yana cewa ba za a fahimci farin jinin gwamnan yadda ya kamata ba idan aka duba shi ta mahangar siyasar manyan ‘yan siyasa kawai.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Tinubu ya gano hanyar kayar da shi a 2027

Israel ya ce wasu daga cikin abokan hamayyar Adeleke sun raina yadda yake iya cudanya da talakawa, musamman saboda yadda suke mai da hankali kan rawa da waka da yake yi a bainar jama’a.

Ya ce maimakon ganin wadannan dabi’u a matsayin nakasu, sun taimaka wa gwamnan wajen kulla alaka ta zuciya da masu kada kuri’a da kuma nuna cewa yana kusa da jama’a.

Abin da APC za ta koya

Sugaban matasan na APC ya gargadi jam’iyyar kan kada ta rika auna ‘yan takara ne bisa karbuwarsu a tsakanin manyan ‘yan siyasa ko matsayinsu a da'irar Abuja kawai.

Israel ya ce nasarar zabe a karshe tana dogara ne kan fahimtar masu kada kuri’a a matakin kasa da kuma amsa bukatunsu.

“Ba a lashe zabe da kason amincewa da ake da shi a Abuja ba. Ana lashe shi ne ta hanyar fahimtar mutane yadda suke,” in ji shi.

Ya ce saboda haka sakamakon Osun ya kamata ya sa APC ta sake duba alakar da ke tsakaninta da masu kada kuri’a, dabarun yakin neman zabe da kuma zabin mutanen da take amfani da su wajen isar da sakon siyasa gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Hanyar da APC za ta bi don lashe zaben gwamnan Osun'

Dayo Israel ya ba APC shawarwari
Dayo Israel na jawabi a wajen wani taro. Hoto: @dayoisrael
Source: UGC

Maimakon kafa wani kwamitin da zai sake rubuta rahoto ba tare da yin sauye-sauye masu ma’ana ba, Israel ya bukaci jam’iyyar ta yi cikakken nazari a cikin gida domin mayar da koma bayan Osun zuwa wata sabuwar dabarar samun nasarar zabe.

Ya ce mutunta masu kada kuri’a tare da koyon darasi daga rashin nasara na da muhimmanci wajen dorewar APC da kuma amincewar jama’a da ita yayin da take shirin shiga zaben kasa na gaba.

Adeleke ya mika bukatarsa ga Oyebamiji

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi muhimmin kira ga abokin hamayyarsa Bola Oyebamiji, na jam'iyyar APC.

Gwamna Adeleke ya ce Bola Oyebamiji ne ya kamata ya kira shi ya taya shi murna, ba shi ne zai kira Oyebamiji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng