Sarki Ya Sha Kunya da Ya Roƙi Kujerar da Gwamna Ya Zauna Kanta a Wurin Ibada

Sarki Ya Sha Kunya da Ya Roƙi Kujerar da Gwamna Ya Zauna Kanta a Wurin Ibada

  • Sarkin Iyin-Ekiti ya nemi a ba shi kujerar da Gwamna Biodun Oyebanji ya zauna a lokacin ibada domin kai ta fada
  • Fadar Oluyin ta ce an bukaci kujerar ne domin kula da ita da kuma gudanar da wasu bukukuwan gargajiya
  • Cocin Anglican ta ki mika kujerar, tana mai cewa an sake fasalinta kuma an hade ta da kayan bagadin cocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Cocin Anglican ta Babamuboni da ke Iyin-Ekiti ta ki amincewa da bukatar wani Sarki a jihar.

Sarkin Iyin-Ekiti, Adeniyi Adeola Ajakaiye ya buƙaci a mika masa wata kujera da Gwamna Biodun Oyebanji ya zauna kanta.

Sarki ya bukaci kujerar da gwamna ya zauna a coci
Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji yayin ziyara a coci. Hoto: Biodun Oyebanji.
Source: Facebook

Sarki ya bukaci kujerar gwamna a coci

Sarkin ya bukaci a kai kujerar da Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi amfani da ita a wani taro na musamman zuwa fadarsa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 da suka sa Adeleke ya tumurmusa APC a zaben Osun

A ranar 31 ga Mayu, 2026, Oyebanji ya halarci bikin cikar Omolade Foluso Bamidele, kanin Opeyemi Bamidele, shugaban majalisar dattawa, shekaru 60.

An gudanar da bikin ne a cocin Babamuboni Memorial Anglican da ke Iyin-Ekiti, kwanaki kadan kafin zaben gwamnan Ekiti na 2026.

Bayan kammala ibadar godiyar, Oluyin na Iyin-Ekiti ya bukaci a ba shi kujerar da gwamnan ya zauna a kanta.

A wata wasika mai kwanan wata 17 ga Yuni, 2026, wadda aka aika wa limamin cocin, fadar Oluyin ta bukaci a kai kujerar fada.

Fadar ta ce za a ajiye kujerar ne domin “kula da ita a matsayin ta sarauta da kuma gudanar da bukukuwan gargajiya da suka dace”.

Wasikar, wadda Elejide Omobulejo, sakataren majalisar Oluyin, ya sanya wa hannu, ta ce majalisar ta yanke shawarar neman kujerar bayan tuntuba.

Ta ce:

“Bayan tuntuba da tattaunawa, majalisar Oluyin-in-Council ta yanke shawarar cewa a gaggauta kai kujerar da lamarin ya shafa zuwa fadar Oluyin.”

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnan Kebbi Ya ajiye mataimakinsa, ya dauko sabon abokin takara

Majalisar ta ce kujerar za ta kasance karkashin kulawar sarauta, tare da gudanar da bukukuwan gargajiya da suka dace.

Ta kuma bukaci a sanya sabuwar kujera da za a samar a karkashin tsauraran matakan tsaro domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari.

Sarki ya bukaci kujerar da gwamna ya zauna a coci
Taswirar jihar Ekiti da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Martanin da cocin ya yi ga bukatar

A wata wasika mai kwanan wata 18 ga Yuni, 2026, cocin ta sanar da fadar cewa ba za ta iya “mika, canja ko cire” dukiyar cocin ba.

Cocin ta ce ba za ta iya mika dukiyar cocin domin wasu ayyukan waje ba, sai an bi hanyoyin da hukumomin addinin Anglican suka tanada.

Ya ce ana gudanar da gyare-gyare da sake fasalin ginin, lamarin da ya sa aka cire kujeru da sauran kayan daki daga wuraren da suke.

Cocin ya ce amincewa da bukatar fadar zai haifar da wasu batutuwan gudanarwa da suka wuce ikon da aka bai wa cocin yankin.

Ya bayyana cewa yayin gyaran ginin, an cire tsofaffin kujeru da sauran kayan daki daga tsarin da suke a baya.

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

Sarki ya mutu a Ekiti

An ji cewa Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi alhinin rasuwar babban basarake wanda ya ba da gudummawa mai yawa.

Marigayin wanda shi ne Alawe na Ilawe Ekiti, Oba Adebanji Alabi ya yi bankwana da duniya ne bayan fama da rashin lafiya.

Oyebanji ya bayyana marigayin a matsayin ma’ajiyar tarihi, ilimi da al’adu, wanda mulkinsa ya kawo zaman lafiya da ci gaba a Ilawe Ekiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.