Takarar Obi da Kwankwaso Ta Gamu da Cikas, Rikicin Shugabanci Ya Raunana Ta

Takarar Obi da Kwankwaso Ta Gamu da Cikas, Rikicin Shugabanci Ya Raunana Ta

  • Rikicin da ke cikin OK Movement ya ɗauki sabon salo bayan rasa wani daga cikin jiga-jigai a tafiyar jam'iyyar NDC
  • An ce darakta-janar na tafiyar ya ce ya yi murabus ne domin ya mayar da hankali kan takararsa ta kujerar Sanatan Kogi ta Gabas a zaɓen 2027
  • Duk da murabus ɗinsa, dan siyasar ya jaddada cewa har yanzu yana goyon bayan Peter Obi, wanda ya kira “shugabana”, tare da kasancewa mai biyayya ga NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rikicin da ke faruwa a cikin 'OK Movement' ya ɗauki sabon salo a ranar Talata kan rikicin shugabanci.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Darakta-Janar na tafiyar, Cif Peter Ameh, ya sanar da murabus dinsa a Abuja.

Darakta janar na tafiyar Kwankwaso, Obi ya yi murabus
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Shugaban tafiyar Obi, Kwankwaso ya yi murabus

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Vanguard, ya ce zai bar mukamin ne domin ya mayar da hankali kan takararsa ta Sanatan Kogi ta Gabas a 2027.

Kara karanta wannan

Da gaske Atiku Abubakar ya janyewa Peter Obi takara saboda zaɓen 2027?

Wannan lamari ya jefa magoya bayan tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar National Democratic Congress, NDC, cikin rudani da rashin tabbas.

Ya rubuta cewa:

“Ina miƙa murabus na a hukumance daga matsayin Darakta-Janar na OK Movement, wanda zai fara aiki nan take.
“Wannan mataki zai ba ni damar ware lokacin da ake bukata da kuma kuzari domin yaƙin neman zaɓena na gundumar Sanatan Kogi ta Gabas, inda nake ɗan takarar Nigeria Democratic Congress, NDC.”
Rikicin shugabanci a tafiyar Obi, Kwankwaso na neman jawo matsala
Jiga-jigan jam'iyyar NDC, Peter Obi, Seriake Dickson, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Seriake Dickson.
Source: Twitter

'Ina nan daram a NDC' - Ameh

Sai dai tsohon Darakta-Janar ɗin ya bayyana cewa murabus ɗinsa ba ya nufin ya rage goyon baya ko biyayyarsa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, wanda ya kira “shugabana”.

Ameh ya ce:

“Cikin tawali’u, zan amince da duk wanda shugabana ya naɗa domin ya gaje ni a wannan matsayi.
“Ina bayyana matuƙar godiyata ga shugabana, Mista Peter Obi, saboda kyakkyawan jagorancinsa, amincinsa da kuma mutuncinsa da ya daɗe yana da shi. Waɗannan halaye ne suka zaburar da kafa OK Movement kuma suka ci gaba da tsara manufofinsa da hangen nesansa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi wa APC yasa a Kano, manya a jam'iyyar sun rungumi Kwankwasiyya

“Har yanzu ina matuƙar jajircewa wajen kare manufofin da suka haɗa mu, kuma ina yi wa OK Movement fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.”

A kwanan nan, tafiyar ta shiga rikicin shugabanci tsakanin ɓangarori, inda wasu mambobi suka yi watsi da jagorancin Ameh.

Yayin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, Movement ɗin zai buƙaci warware rikicin shugabancinsa cikin gaggawa idan yana son ci gaba da kasancewa mai tasiri a siyasar ƙasar.

Peter Obi ya ba yan siyasa shawara

Mun ba ku labarin cewa Peter Obi ya bukaci ’yan siyasa su tabbatar da cewa babu dan Najeriya da ya rasa ransa saboda zabe a shekarar 2027.

Dan takarar na NDC ya ce ya kamata ’yan takara su yi kamfen bisa batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya.

Obi ya bukaci a gudanar da zabe inda kuri’un jama’a za su yi tasiri, yana mai cewa makomar ’yan Najeriya ta dogara da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.