Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Yarin Bakura ya raba gardama kan batun jagorancin APC a jihar Zamfara
  • Ya bayyana cewa, gwamna Matawalle shi ne a hukumance ya kamata ya jagoranci jam'iyyar a jihar
  • Ya bayyana dalilansa daga tsarin jagoranci na jam'iyyar ta APC tare da amincewa da jagorancin Matawalle

Tun bayan da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya koma jam'iyyar APC, shugaban riko na jam'iyyar Maimala Buni ya sanar da nadin gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Bayyana Matawalle a matsayin jagoran jam'iyyar APC ya jawo fushi ga wasu jiga-jigan 'yan siyasar jihar Zamfara, wadanda suka hada da, tsohon gwamna Abdulaziz Yari da tsohon dan majalisar dattawa Kabiru Marafa yayin da suka ki amincewa da nadin.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Yariman Bakura, ya bayyana amincewarsa da nadin, tare da bayyana dalilai daga tsarin mulkin jam'iyyar APC.

KARANTA WANNAN: Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu

Yariman Bakura Ya Magantu Kan Rikicin da Ya Kunno Kai a APC a Jihar Zamfara
Tsohon gwamnan jihar Zamfara Yariman Bakura | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya bayyana matsayarsa game jagorancin gwamna Matawalle da kuma yadda ya kasance uban siyasa a jihar.

A cewarsa:

"Duk wani dan jam'iyyar APC na Zamfara a yanzu, ko ya amince, ko ya fada ko bai fada ba tsarin mulki ya ba Dakta Bello Muhammad Matawalle jagoranci.
"Don haka dukkanmu, tun daga ni har zuwa kan duk wanda kake gani a Zamfara indai zai yi siyasar APC, to yana karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara na yanzu.

KARANTA WANNAN: Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

Da yake bayyana dalilin ba gwamna Matwalle jagorancin jam'iyyar, Bakura yace:

"A tsarin mulkin jam'iyyar APC ta Najeriya, jagoran jam'iyya na tarayya shine shugaban kasa, a yau Alhaji Muhammadu Buhari. A kowace jiha, jagoran wannan jam'iyya shine gwamnan wannan jiha.
"Don haka shi yasa lokacin da shugaban jam'iyya na rikon kwarya ya tafi a Zamfara, yace daga yau ya dakatar da dukkanin shugabannin jam'iyya na jihar Zamfara, an sauke su, kuma jagoranci ya koma ga gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Muhammad Matawalle."

Jagoran APC a Zamfara: Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle ba

Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, da Sanata Kabiru Marafa, sun yi tur da batun cewa Gwamna Bello Matawalle ne shugaban APC a jihar.

Jiga-jigan na Jam’iyya mai mulki sun bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni.

Idan za ku tuna, Shugaban riko na APC, Mai Mala Buni ya ayyana Gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar Zamfara bayan ya sauya sheka daga PDP.

PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

A wani labarin daban, Gabanin shirin sauya shekar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP, zuwa APC, babbar jam'iyyar adawar (PDP) ta gargadi gwamnan kan wannan matakin, tare da barazanar yin mai yiwuwa don kare dokokin jam'iyya.

PDP ta gargadi Bello Matawalle da ya sani cewa take-takensa sun yi daidai da shawarar barinsa kujerar mulki saboda an zabe shi a karkashin jam'iyyar PDP, jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar PDP:

"Babu wata doka da ta ba shi damar tsallakewa zuwa wata jam’iyya tare da mukamin gwamna da aka ba PDP ta hanyar zabe, kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma hukuncin Kotun Koli.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel