Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi ram da wasu da ake zargin suna aikata luwadi a wata unguwa
  • An cafke mutanen ne su biyar bayan samun rahoton abubuwan da suke aikatawa a cikin unguwar
  • Hukumar Hisbah ta bayyana godiya ga jama'ar yankin tare da yaba wa masu ruwa da tsaki na yankin

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata luwadi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso.

Shugaban hukumar Harun ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, BBC ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta tattaro, a cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

KARANTA WANNAN: Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

An kwamushe wasu da ake zargi da aikata luwadi a jihar Kano
Taswirar jihar Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Harun ya ce:

"Duka wadanda ake zargin sun haura shekara 20, mun kuma kama su ne a ranar 11 ga watan Yuli a wani samame na musamman."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Shugaban hukumar ya nuna rashin jin dadi kan wadannan matasa da aka kama.

Ibn-Sina ya yi wa 'yan yankin godiya da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da suka bayar da hadin kai wajen kama wadannan mutane.

Ya ce za a mika wadannan mutane da aka kama zuwa kotu.

‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, an samu hatsaniya, a Egbe, Ikotun dake jihar Legas, inda wasu masu luwadi sukayi fada da junansu bayan kmauwa da cutar kanjamau.

Ezeugo daya daga cikin masu luwadin shine ya sanyawa masoyin nasa cutar, bayan ya kawo wani zaiyi luwadin dashi sai na farkon ya tayarda hayaniya a cikin gidan da misalin karfe 3 na dare a ranar Talata.

Mutanen Unguwa dole tasa suka kirawo jami’an ‘Yan Sanda na Ikotun, inda suka kama wadanda ake zargin. Inda Ezeugo ya masawa hukumar ‘Yan Sanda cewa ya kai shekara biyar yana luwadi.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

KARANTA WANNAN: Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dakatar da kungiyar manyan mataimaka ta musamman a Kano saboda rikicin shugabanci, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce gwammnati ta lura cewa abubuwan dake gudana a kungiyar suna dauke musu hankali daga asalin ayyukansu da kuma ba da gudunmawarsu ga gwamnati.

Ya ce rashin jituwar da ke tsakanin shugabannin biyu na kungiyar ya haifar da rashin jin dadi da kunya ga gwamnati wanda in ba a kula ba, za ta iya lalata manufofi da burin da aka sanya kan SSA din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel