Ahmed Ibrahim Lawan
Mun ji cewa Shugaba Buhari ya kai bashin da ke wuyan Najeriya ya lula sama. Sanata Muhammad Enagi Bima wanda shi ne Sanatan Neja ta Kudu ya bayyana mana wannan.
Shugaban Majalisar Tarayya Ahmad Lawan ya koka da shirin da aka yi wa Coronavirus bayan ga halin da asibitin UNIABUJA ya ke, ya ce akwai sauran aiki wajen yakar Annobar Coronavirus.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai bukatar yan Najeriya su dage wajen gudanar da addu’o’i ga shuwagabanninsu domin shuwagabannin su samu daman yi musu aiki yadda ya kamata.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Injiniya Ahmed Kadi Amshi a matsayin shugaba hukumar da ke kula da majalisar dokokin tarayya, sannan ya kuma kaddamar da wasu 11 a matsayin mambobin hukumar.
Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura wanda tsohon Sanatan Zamfara ne, ya ce albashi da alawus din Majalisa ya yi daidai. A cewarsa, albashin Majalisa bai yi yawa ba.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da samun rahoton barazanar kai ma majalisar dokokin Najeriya hari da wasu miyagun yan ta’adda suke shirin kaiwa.
Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, ta tabbatar da nadin Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu a matsayin darakta janar na hukumar jiragen sama na Najeriya wato NCAA.
An cire Ahmad Lawan, an nada wanda zai jagoranci kwamitin sulhun APC, Saboda ana zargin cewa Ahmad Lawan da Idris Wase manyan Magoya-bayan Adams Oshiomhole ne.
Ahmad Lawan ya ja kunnen MDAs a game da mika rahoton binciken kudinsu na bara. Shugaban majalisar ya nunawa ma’aikatu su na da damar hana su kasafin kudin bana.
Ahmed Ibrahim Lawan
Samu kari