Wurin kula da masu dauke da cutar Coronavirus a Abuja ba su da kyau – Lawan
Shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan, ya nuna damuwa game da halin da dakunan killace masu dauke da cutar Coronavirus su ke ciki a Abuja.
A jiya Mai girma Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana cewa ba a kammala aikin da ya dace a dakunan kula da cutar Coronavirus da ke babban birnin tarayyan kasar ba.
Dr. Lawan ya yi wannan magana ne a Ranar Laraba lokacin da ya zagaya domin ganewa idonsa halin da dakunan da ke cikin asibitin koyon aiki na jami’ar Abuja su ke ciki.
Shugaban Sanatocin ya ke cewa har yanzu akwai sauran aiki sosai a wadannan dakuna da ke cikin asibitin koyar da Likitoci na jami’ar tarayya da ke Garin Gwagwalada.
Lawan ya ce: “Daga binciken da mu ka yi a can, mun gano cewa dakunan wucin-gadin da aka ware ba su da kyau; ba su yi kamata da wurin da za a karbi maras lafiya ba.”
KU KARANTA: Cutar Coronavirus ta sa kasafin kudin Najeriya ya shiga wala-wala
“Ina ganin cewa wannan abu ne da ya kamata ace an gyara daga yanzu zuwa gobe.” Idan ba ku manta ba ‘Dan Italiyan da aka tsare ya koka da halin da ya shiga ciki a Legas.
“Mu na cikin wani hali ne na kar-ta-kwana, ko da ba mu samu wadanda su ka kamu da cutar ba; bai kamata mu sakata ba. Dole mu yi bakin kokarinmu na gyara dakunan asibitin.”
“Bai kamata ace Najeriya da ta fi kowace karfin tattalin arziki a Afrika mai yawan al’umma miliyan 200, amma ace a babban birnin tarayya babu dakin killace maras lafiya.”
Sanatan ya nuna cewa za a iya samun wanda wannan cuta za ta fada kansa, kuma ya zama babu inda za a kula da shi a kaf Yankin, Ahmad Lawan ya ce ba za mu karbi wannan ba.
“Babu hasken wuta, babu injin bada wutan lantarki. Akwai na’urorin AC biyu ko uku da aka kawo.” A karshe Lawan ya bukaci Minista ta saki kudin da aka warewa NCDC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng