Sulhu: APC ta saduda, ta maye gurbin Ahmad Lawan da Bisi Akande

Sulhu: APC ta saduda, ta maye gurbin Ahmad Lawan da Bisi Akande

Shugabannin jam’iyyar APC sun sake duba lamarin kwamitin sulhun rikicin cikin-gida, inda su ka cire Ahmad Lawan a matsayin shugaban kwamitin, su ka nada Bisi Akande.

A Disamban 2019, majalisar NWC ta bada sanarwar cewa Sanata Ahmad Lawan zai jagoranci maganar sulhu a jam’iyyar. Yanzu Cif Bisi Akande aka ba nauyin wannan aiki.

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, shi ne ya nuna bai cewa bai gamsu da Ahmad Lawan da Idris Wase ba domin kowa ya san cewa su na cikin yaran Adams Oshiomhole.

A Ranar Litinin, 10 ga Watan Fubrairun 2020, Mallam Lanre Issa-Onilu ya sanar da cewa shugaba Buhari da shugabannin APC sun yi wa kwamitin sulhun jam’iyyar garambawul.

Lanre Issa-Onilu ya ce kwamitin da aka kafa yanzu ya kunshi:

1. Cif Bisi Akande

2. Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello

3. Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola

4. Shugaban masu rinjaye a Majalisa, Yahaya Abdullahi

5. Mataimakin Shugaban majalisar wakilai, Hon. Ahmed Idris Wase

KU KARANTA: Shugabannin Mazabu sun koma jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara

Sulhu: APC ta saduda, ta maye gurbin Ahmad Lawan da Bisi Akande
Cif Bisi Akande zai dinke barakar da ke cikin Jam'iyyar APC
Asali: UGC

6. Sanata Umaru Tanko Al-Makura

7. Sanata Kashim Shettima

8. Karamar Ministar muhalli, Sharon Ikeazor

9. Alh. Nasiru Aliko Koki

10. Sanata Khairat Gwadabe-Abdulrazak

11. Sanata Binta Garba

12. Sanata John Enoh

Shugaban jam’iyyar APC na farko a tarihi, Cif Bisi Akande shi ne zai shugabanci wannan kwamiti. Sanata John Enoh ne zai yi aiki a matsayin Sakataren kwamitin inji Malam Issa-Onilu.

An ba kwamitin alhakin sasanta duk barakar da ta ke cikin gidan APC, inda za ta zauna da fusatattun ‘Ya ‘yanta fadin Najeriya domin ganin an shawo karshen duk wata rigima.

Issa-Onilu ya ce za a kaddamar da wannan kwamiti ne a yau Talata, 11 ga Watan Fubrairu a Sakatariyar jam’iyyar a Abuja. Da karfe 3:00pm za a kaddamar da wannan kwamiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel