Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Kyaftin Nuhu a matsayin Shugaban NCAA

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Kyaftin Nuhu a matsayin Shugaban NCAA

- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu a matsayin darakta janar na hukumar kula da zirga-zirgan jiragen sama na Najeriya wato NCAA

- Ta tabbatar da nadin ne a yau Talata, 18 ga watan Fabrairu a zaman majalisar

- Hakan ya biyo bayan rahoton tantancewa da kwamitin majalisar dattawa kan jiragen sama, karkashin jagorancin Sanata Smart Adeyemi ta gabatar a zauren majalisar

Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, ta tabbatar da nadin Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu a matsayin darakta janar na hukumar kula da zirga-zirgan jiragen sama na Najeriya wato NCAA.

Hakan ya biyo bayan rahoton tantancewa da kwamitin majalisar dattawa kan jiragen sama, karkashin jagorancin Sanata Smart Adeyemi ta gabatar a zauren majalisar a Abuja.

A baya Legit.n ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kyaftin Musa Nuhu a matsayin sabon Direkta-Janar na Hukumar Kula da Zirga-Zirgan jiragen Sama ta Kasa, NCAA.

Mista Nuhu zai maye gurbin Kyafyin Mukhtar Usman a matsayin shugaban hukumar kamar yadda sanarwar da Jami'in Hulda da Al'umma na hukumar, James Odaudu ya fitar.

Mista Odaudu ya ce, "Kafin nadin Nuhu, shi ne wakilin Najeriya na dindindin a kungiyar kasa da kasa da sufurin jiragen sama, kuma matukin jirgin sama ne kana kwararre kan fanoni daban-daban a bangaren aikin jiragen sama."

Sabon shugaban na NCAA yana da digiri ta biyu (MSc) a fanin kasuwancin sufurin jiragen sama kuma yana daya daga cikin matukan jirage a tawagar shugaban kasa a matsayin Kyaftin.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya za ta shuka itatuwa miliyan 30 a 2020

A gefe guda kuma, mun ji cewa wani rahoto daga kungiyar taimakon kai da kai mai suna Center for Information Technology and Development (CITAD) ta ce a tarihin majalisar dattijan Najeriya, mata 36 kadai suka taba samun zama sanatoci tun 1999, kamar yadda jaridar The Nation online ta ruwaito.

Rahoton CITAD din ya bayyana ne a wani taron horar da manema labarai da ta shirya a birnin Yola da ke jihar Adamawa. Kungiyar ta ce tun daga 1999 majalisar tarayyar ta samu mambobi 654 ne kuma gurbi 618 maza suka cike shi inda matan suka ciki 36.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel