Ome Agege: Kusan rabin mutanen Najeriya su ke lullube da talauci
Mun samu labari cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ovie Omo-Agege, ya yi magana game da halin masifar talaucin da ake fama da ita a kasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa Ovie Omo-Agege ya yi wannan magana ne a lokacin da wasu wadanda su ka halarci Makaranta tare su ka shirya bikin cika shekaru 50 da yaye.
A Ranar Asabar da ta wuce ne ‘Daliban makarantar Sojojin Najeriya ta NMS da ke Zariya su ka yi wannan biki wanda ya zama hanyar sake haduwa da ‘Daliban shekarar 1979.
Sanatan na APC ya ce rabin ‘Yan kasar nan, su na zaune ne a cikin talauci. Alkaluma dai sun nuna cewa akwai Talakawa fiye da miliyan 86 a Najeriya da ba su da wani hali.
Da ya ke magana game da adadin wadanda ke cikin talauci a Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege, ya nuna cewa burin gwamnati shi ne ta ceto mutane 100 a shekaru goma nan gaba.
KU KARANTA: Yadda wani Bawan Allah ya auri Mata har 58 a Duniya
“Wannan bai dace ba, kuma burinmu shi ne a fito da mutane miliyan 100 daga cikin kangin talauci a cikin shekaru 10. Wannan da kamar wuya, amma ba zai gagara ba.”
“Kasar Indiya ta ceto mutane miliyan 170 daga cikin talauci tsakanin shekarar 1990 zuwa 2013, inda ta rage adadin masu fama da masifar talauci a kasar da kashi 25%.”
“China da Indonesiya su na cikin kasashe 17 na farko a Duniya da su ke fitar da miliyoyin mutane daga halin fatara. Idan Indiya da Indonesiya za su iya, Najeriya za ta iya.”
“Amma dole ana bukatar manufofi masu karfi da za su sauya fasalin tattalin arzikinmu da yadda mu ke rayuwa. Akwai bukatar mu samo hanyoyin magance matsalolinmu.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng