Barazanar kai ma majalisa harin ta’addanci gaskiya ne – shugaban majalisa

Barazanar kai ma majalisa harin ta’addanci gaskiya ne – shugaban majalisa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da samun rahoton barazanar kai ma majalisar dokokin Najeriya hari da wasu miyagun yan ta’adda suke shirin kaiwa.

Daily Trust ta ruwaito Lawan ya koka ne a ranar Talata, 18 ga watan Feburairu, yayin ganawa da shuwagabannin tsaro, inda yace mutane da dama da ba’a san ko su wanene ba, suna shige da fice a majalisar ba tare da samun takardar gayyata ba.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Dan jaridar dake da hannu cikin satar N2.5bn ya yanke jiki ya mutu

Lawan ya bayyana ma mahalarta taron cewa shi da kansa ya samu rahoto daga hukumar tsarp ta DSS dangane da yiwuwar samun hare hare a majalisar, don haka ya nemi hukumomin tsaro su karfafa tsaro a majalisar domin kawar da yiwuwar kowanne irin hari.

Mai magana da yawun shugaban majalisar, Ola Awoniyi, yace Lawan ya gargadi jami’an tsaron kamar haka; “Duk jami’in tsaron da muka ba shi aikin tabbatar da tsaro, sai kuma muka kama shi da hannu cikin wata matsala, za mu tabbata an hukunta shi.

“Dolene a yanzu mu yi aiki tare, idan ma ta kama hukumomin tsaro su yi ma jami’ansu dake aiki a nan magana ne sai a yi, saboda gaskiyar zance shi ne muna cikin hadari, a duk lokacin da ka zo majalisa sai ka gansa a cike kamar kasuwa.” Inji shi.

Lawan yace duba da karuwar matsalolin tsaro a Najeriya, dolene a baiwa majalisa tsaro na musamman domin yan majalisu masu yin dokoki su samu daman gudanar da aikinsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Daga karshe Lawan yace duk wanda ba shi da wani abin yi a majalisa, bai kamata ya je majalisa ba, amma idan har mutum yana da kwakkwaran dalilin zuwa majalisa, jami’an tsaro zasu iya kyale shi ya shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel