Wasu 'Yan Takarar Gwamna na Kashe Naira Biliyan 20 zuwa 30 don Su Ci Zabe a Najeriya
- Shugaban EFCC na kasa ya ce wasu masu neman kujerar gwamna na kashe tsakanin Naira biliyan 20 zuwa 30 wajen neman nasara a zabe
- Ola Olukoyede ya gargadi cewa hakan na haifar da karuwar cin hanci da karkatar da kudaden gwamnati a Najeriya
- Hukumar EFCC ta ce ta kama tare da gurfanar da mutane da dama kan laifuffukan da suka shafi sayen kuri'u a lokacin neman takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya fallasa yadda 'yan takarar gwamna ke kashe makudan kudi a Najeriya.
Olukoyede ya bayyana cewa wasu masu neman takarar gwamna a Najeriya na kashe tsakanin Naira biliyan 20 zuwa 30 domin samun nasara a zabe.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta rahoto cewa Olukoyede ya yi wannan bayani ne a jihar Kwara, yayin gabatar da lakca a Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Tsare-tsare (CPSS) ta Jami'ar Ilorin.
EFCC ta nuna damuwa kan kudin zabe
A laccar mai taken "Tabbatar da zaman lafiya da sahihin zaben 2027 a Najeriya", shugaban EFCC ya ce yawan kudaden da ake kashewa wajen neman mulki na zama babbar barazana ga dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa idan 'dan siyasa ya kashe makudan kudade kafin ya samu mulki, akwai yiwuwar ya fara neman hanyoyin dawo da kudin bayan ya shiga ofis.
A cewarsa, hakan ne ke jefa shugabanni cikin laifuffukan karkatar da kudaden gwamnati maimakon mayar da hankali kan yi wa jama'a hidima.
Illar sayen kuri'u a zabukan Najeriya
A ruwayar Leadership, Olukoyede ya ce sayen kuri'u da amfani da kudi wajen jawo ra'ayin masu zabe na raunana tsarin shugabanci nagari.
Ya ce:
"Shugabannin da suka sayi hanyar shiga ofis sun fi karkata wajen dawo da kudin da suka kashe maimakon kula da muradun jama'a."
Ya kara da cewa hukumar EFCC na ci gaba da yaki da duk wani nau'in cin hanci da rashawa da ka iya gurbata tsarin zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya

Source: Twitter
Jami'an EFCC sun kama masu sayen kuri'u
Shugaban EFCC ya bayyana cewa hukumar ta kama mutane da dama a sassa daban-daban na kasar nan saboda sayen kuri'u da sauran laifuffukan zabe.
Ya ce wasu daga cikin wadanda aka gurfanar a kotu kan wannan laifi sun hada da: 'yan siyasa, jami'an zabe da talakawan da aka samu da hannu a laifuffukan zabe.
Ya jaddada cewa babu wanda zai fi karfin doka idan aka same shi da hannu wajen karya dokokin zabe.
EFCC ta kama Saleh Mamman a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta sanar da cafke tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, bayan hukuncin da kotu ta yanke masa.
Tun farko dai babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukunci kan laifin karkatar da makudan kudade yayin da yake rike da mukamin minista.
Shugaban EFCC ya bayyana cewa kamun tsohon ministan wani muhimmin mataki ne da ke nuna kudirin gwamnatin tarayya na yaki da cin hanci da rashawa.
Asali: Legit.ng
