COVID-19: ‘Yan Majalisa su na tantamar bada albashin Maris a matsayin gudumuwa

COVID-19: ‘Yan Majalisa su na tantamar bada albashin Maris a matsayin gudumuwa

An taso ‘Yan majalisar tarayya a gaba a Najeriya da su bada daukacin albashinsu na Watan Maris a matsayin gudumuwarsu domin yaki da muguwar cutar nan ta Coronavirus.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an bukaci ‘Yan majalisar su yi hobbasa ne bayan ganin Ministocin kasar sun bada 50% daga cikin albashinsu na wannan Watan na Maris.

Kwanakin baya Honarabul Mansur Manu Soro mai wakiltar Ganjuwa da Darazo a majalisa ya yi kira ga Abokan aikinsa su hakura da albashin domin su tara gudumuwar N360m.

Kungiyoyi irinsu CHRICED da GGT sun nuna cewa akwai bukatar Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai su fito su nuna kishi su bada gudumuwa domin kauda wannan annoba.

Sanata Betty Apiafi ta shaidawa jaridar cewa gudumuwarsu ba za ta yi wani tasiri a wannan yanayi ba, inda ta ce abin da ya fi kamata shi ne gwamnatin tarayya ta fito da kudi.

KU KARANTA: Kyari, Bala, El-Rufai, Babandede, su na dauke da cutar Coronavirus

COVID-19: ‘Yan Majalisa su na tantamar bada albashin Maris a matsayin gudumuwa
Mutane sun bukaci ‘Yan Majalisa su kashe albashinsu wajen maganin annoba
Asali: Twitter

Sanata Apiafi ta ke cewa Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai su na kashe makudan kudi a kan mutanen Mazabarsu saboda irin yunwar da ake ciki a Najeriya a halin yanzu.

Honarabul Benjamin Kalu wanda ke magana a madadin ‘yan majalisar wakilan tarayya ya nuna cewa zaftare albashinsu ya na nufin rufe kokarin alherin da su ke yi wa jama’a.

Benjamin Kalu ya ce da mutane sun san albashinsu, da ba su bukaci su bada gudumuwar rabin wannan kudi a Watan nan ba. Kalu ya ce rabin albashinsu ba zai kai ko ina ba.

Sanata Muhammad Adamu Bulkachuwa ya nuna cewa zai yi irin na shi taimakon. Shi ma Sanata Bulus K. Amos da wasu ‘Yan majalisa su na goyon bayan a bada gudumuwar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng