Za ayi bincike game da ingancin takardar umarnin Abba Kyari – Majalisar Wakilai

Za ayi bincike game da ingancin takardar umarnin Abba Kyari – Majalisar Wakilai

Rahotanni sun ce majalisar wakilan tarayya ta tabbatar da cewa ta na bincike a game da wata wasika da ake tunanin ta fito daga ofishin Abba Kyari a fadar shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ‘yan majalisa su na bincike tare da duba ingancin takardar da ake zargin Abba Kyari ya aikowa shugabanta Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.

Jama’a sun ga wannan takarda da ake kyautatata zaton fadar shugaban kasa ta aikowa Kakakin majalisar a game da matakan da ya kamata a dauke game da cutar COVID-19.

Ko da cewa wannan takarda ta sirri ce, mun ji labari mutane sun ci karo da ita a shafukan sada zumunta irinsu Facebook da kuma Tuwita a cikin farkon wannan makon.

A wannan wasika, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya zargi wasu ‘Yan majalisa da kin bari a duba su yayin da su ka iso filin jirgin saman Najeriya daga kasashen waje.

KU KARANTA: Coronavirus: Dangote ya bukaci Ma'ikata su rika aiki daga gidajensu

Za ayi bincike game da ingancin takardar umarnin Abba Kyari – Majalisar Wakilai

Majalisar Wakilai ta na binciken takardar da Kyari ya rubuta mata
Source: Twitter

Da Jaridar ta tuntubi Mai magana da yawun bakin ‘Yan majalisar wakilai watau Hon. Benjamin Kalu, ya shaida mata cewa: “Har yanzu mu na binciken sahihancin takardar.”

Benjamin Kalu mai wakiltar Mazabar Bende na jihar Abia a karkashin jam’iyyar APC mai rinjaye ya bayyana cewa an duba shi a filin jirgi bayan ya dawo daga Dubai kwanaki.

Kalu ya yi wannan bayani ne da aka tuntubesa a WhatsApp. A cewarsa, akasin abin da Kyari ya fada, ma’aikatan da ke yaki da cutar Coronavirus sun duba shi a filin jirgi.

A wannan wasika shugaban ma’aikatan na fadar shugaban kasa Buhari ya aikowa Kakakin majalisa, an yi kuskuren kiran Gbajabiamila da shugaban majalisar dattawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel