Mark Okoye, Shugaban Hukumar SEDC da Ya Kama Hayar Ofis kan N153m a Abuja
- Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban SEDC Mark Okoye domin ya kare kansa kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗen kasafin hukumar na 2025
- Kwamitin majalisa ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda aka kashe Naira miliyan 153 wajen hayar ɗaki ɗaya na ofis a birnin Abuja
- Majalisa ta ba shugaban hukumar umarnin kwo cikakkun takardun shige da ficen kuɗaɗe don tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen cikin gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A ranar Talata, majalisar dattawa ta titsiye shugaban hukumar raya shiyyar Kudu Maso Gabas (SEDC), Mark Okoye.
Majalisar ta titsiye Mark Okeye ne kan zargin rashin ingantaccen bayani game da yadda aka kashe kudi har Naira biliyan 16.6 da hukumar ta karɓa daga kasafin 2025.

Source: Twitter
Majalisa ta titsiye shugaban hukumar SEDC
Kwamitin majalisar dattawa mai kula da hukumar SEDC, wanda Sanata Orji Uzor Kalu (Abia ta Arewa) ke jagoranta ne ya titsiye Okeye, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: An shiga rudani kan yanayin da wani babban jami'in Kwastam ya rasu a Bauchi
Majalisar ta nuna rashin jin daɗi musamman kan Naira miliyan 153 da hukumar ta ce ta kashe wajen hayar ofishi mai daki guda a Abuja, da kuma Naira biliyan 2.5 da aka saka a matsayin “kashe-kashen da ba a fayyace ba.”
Matsala ta fara ne ga shugaban SEDC da manyan jami’an hukumar yayin da kwamitin ya duba rahoton kuɗi da suka gabatar a zaman binciken da aka yi.
‘Yan kwamitin sun bayyana ɓacin rai kan yadda Mark Okeye ya gaza yin cikakken bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka karɓa, inda suka sha alwashin tabbatar da cewa an yi amfani da su yadda ya dace.
Majalisa ta samu bayanai daga CBN
Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa CBN ya tabbatar musu har yanzu Naira biliyan 13 cikin N16.6bn da SEDC ta karɓa a watan Disambar 2025 na nan, wanda ke nufin an riga an kashe Naira biliyan 3.6.
“Wannan kwamitin bai gamsu da rahoton kuɗin da aka gabatar ba, kuma ba za mu amince da shi ba,” in ji Kalu.
Sauran ‘yan kwamitin da suka haɗa da Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu), Sanata Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya), da Sanata Austin Akobundu (Abia ta Tsakiya) sun jaddada rashin gamsuwa da rahoton.

Source: Twitter
An ba SEDC wa'adin yin bayani
Sai dai shugaban na SEDC ya kare kansa, yana mai cewa an kashe kudaden ne cikin tsari da kuma bin ka’ida domin aiwatar da ayyukan da suka fi muhimmanci.
“Mun mayar da hankali ne wajen tabbatar da cewa ana amfani da albarkatun da ake da su wajen ayyukan da suka fi muhimmanci. Mun yi komai ta yadda muka tabbatar da cewa akwai kuɗin aiwatar da kwangiloli."
- Mark Okeye.
Sai dai, kwamitin majalisar bai gamsu da bayanansa ba, inda ya umarci hukumar da ta gabatar da cikakkun takardu da suka haɗa da bayanan kwangiloli, bayanan biyan kuɗi da dukkan hujjoji kafin ranar 23 ga wannan watan nan.
Tinubu ya kori shugaban SEDC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin wasu mutane huɗu da ya naɗa muƙamai a hukumar raya yankin Kudu maso Gabas (SEDC).
Onanuga ya ce Tinubu ya kuma maye gurbin dukkanin manyan daraktoci uku da aka naɗa da farko tare da naɗa ƙarin daraktoci guda biyu.
Sauyin ya zo ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan Tinubu ya miƙa jerin sunayen waɗanda aka naɗa a hukumomin SEDC da NWDC ga majalisar dattawa domin tantancewa.
Asali: Legit.ng

