Ahmad Lawan ya ja kunnen MDAs su gabatar da rahoton kashe kudin 2019

Ahmad Lawan ya ja kunnen MDAs su gabatar da rahoton kashe kudin 2019

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce majalisar tarayya za ta dauki mataki a kan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Dr. Ahmad Lawan ya bayyana cewa duk ma’aikatun gwamnati da su ka gaza mika cikakken rahoto game da kashe-kashen kudinsu, za su fuskanci fushinsu.

Kamar yadda mu ka samu labari, an yi wannan magana ne a Ranar 4 ga Watan Fubrairun 2020 a zauren majalisa bayan an amince da kasafin hukumar kwastam.

Idan ba ku manta ba a Ranar Talata ne ‘Yan majalisa su ka amince da kasafin kudin da aka yi wa hukumar kwastam na Naira biliyan 238 a wannan shekarar.

Ahmad Lawan ya ja-kunnen hukumomi da ma’aikatun ne jim kadan bayan Majalisar wakilai ta yi irin wannan gargadi a wani zama da aka yi a makon nan.

“Mu na sa rai MDAs su gabatar da rahoton binciken kudinsu kafin karshen shekara, musamman daf da Watan Disamba ko kuma akalla a farkon wata shekara.”

KU KARANTA: Minista Amaechi ya yi magana game da tallafawa Mata

Ahmad Lawan ya ja kunnen MDAs su gabatar da rahoton kashe kudin 2019
Sanata Ahmad Lawan ya ce dole MDAs su fadi inda su ka kai kudinsu
Asali: Twitter

Ahmad Lawan ya cigaba da cewa: “Wannan idan ya kunshi duka watannin shekara kenan.”

Ya ce: “Idan wata hukumar gwamnati ta ki yin hakan, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba; mu na da damar daukar babban mataki wajen kason kasafin kudi.”

“Domin kuwa dole ka yi bayanin yadda ka kashe kudin shekarar da ta gabata. Don haka ina ba ma’aikatu shawara su bada rahoton abin da su ka yi da kudinsu.”

Shugaban majalisar ya nunawa ma’aikatu su na da damar hukunta wadanda su ka sabawa ka’ida. Sanata Na-Allah ya na cikin wadanda su ka yi magana a zaman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel