Sace Dalibai: Gwamna Ya Umarci Rufe Makarantu bayan Samun Rahoton DSS
- Wani rahoton sirri daga hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ya yi gargaɗin cewa wasu da ake zargi da ta'addanci na shirin sace ɗalibai
- Bayan samun rahoton, gwamnatin Edo ta rufe wasu makarantun sakandare uku da ke ƙaramar hukumar Akoko-Edo domin kariya
- Jami'an DSS sun tabbatar da sahihancin takardar, suna mai jaddada muhimmancin ɗaukar mataki kan bayanan sirri na tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Wani rahoton sirri da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta fitar ya yi gargaɗin yiwuwar sace ɗalibai da yawa a Edo.
Rahoton ya jawo fargaba mai tsanani a jihar da tuni take fama da yawaitar garkuwa da mutane da matsalolin tsaro.

Source: Twitter
Musabbabin rufe makarantun sakandare a yankin Edo
Bayan fitowar rahoton, Gwamnatin Edo ta ba da umarnin rufe makarantun sakandare uku a ƙaramar hukumar Akoko-Edo, cewar Premium Times.
Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 9 ga Yuni, 2026 da muke ciki.
Takardar sirrin ta nuna cewa wasu da ake zargi da kasancewa 'yan bindiga suna shirin kai hari kan makarantu.
An ce hankalinsu ya fi karkata ne kan makarantun da ke yankin Edo ta Arewa domin yin garkuwa da ɗalibai.
Bayanan sirri sun nuna cewa mutanen sun yanke wannan shawara ne bayan gazawar sace attajirai don samun kuɗin fansa.
Sun yi imanin cewa sace ɗalibai zai ja hankalin gwamnati tare da ƙara yiwuwar samun kuɗaɗen fansa masu yawa.

Source: Original
Ana zargin wani na leken asirin makaranta
Rahoton ya kuma bayyana cewa an kama wani matashi mai suna Emmanuel Momidu mai shekara 25 da zargin leƙen asirin makaranta.
An kama shi ne a ranar 4 ga Yunin 2026 yayin da ake zargin yana sintiri a kusa da Makarantar Sakandaren Makeke.
DSS ta ba da shawarar ƙara tsaro a makarantu tare da haɗa kai da 'yan banga da mafarauta na cikin al'umma.
Jami'an DSS sun tabbatar da sahihancin takardar, amma sun nuna damuwa kan yadda aka fitar da ita ga jama'a, cewar Daily Post.
Sun ce irin waɗannan bayanan ana rabawa hukumomin tsaro ne domin dakile hare-hare, ba don yaɗa su a bainar jama'a ba.
Lamarin ya zo ne yayin da mazauna Edo ke ƙara nuna damuwa kan yawaitar garkuwa da mutane a faɗin jihar.
A nasa ɓangaren, Gwamna Monday Okpebholo ya zargi wasu yan siyasa da hannu a ɗaukar nauyin matsalar tsaron jihar.
An gano bukatar yan bindiga a Oyo
Tun farko, mun ba ku labarin cewa Shugabar makarantar da aka sace dalibai a Oyo ta ce masu garkuwar ba su nemi Naira biliyan ɗaya ba kamar yadda ake fada a baya.
Haka kuma ta yi magana a kan cewa 'yan bindigan sun nemi lallai sai an kafa tsarin Shari'ar Musulunci a Najeriya.
Ta bayyana ainihin abin da masu garkuwa da mutanen suka ce suna bukatar a yi masu kafin a sako dalibai da makaman da aka sace.
Asali: Legit.ng

