Yadda Miji da Mata Suka Tafka Damfarar kusan N2bn da Matakin da EFCC Ta Dauka

Yadda Miji da Mata Suka Tafka Damfarar kusan N2bn da Matakin da EFCC Ta Dauka

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wani mutumin da ke ikirarin shi boka ne tare da matarsa kan zargin damfarar kusan N2bn
  • Ana zargin miji da matar sun karbi biliyoyin kudin da sunan za su aiwatar da wata kwangila daga hannun wata bazawara a Delta
  • Kotun tarayya da ke Ado-Ekiti ta umarci a ma'auratan yayin da aka ba EFCC izinin kwace wasu kadarori da suka saya daga kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ekiti - Hukumar EFCC ta gurfanar da wani da ke ikirarin shi boka ne, Olorunbukunmi Taiwo, tare da matarsa, Awolegan Omolola Omotola, kan zargin damfarar kudi da suka kusan Naira biliyan biyu.

An gurfanar da ma’auratan ne a gaban Mai shari’a Abubakar Usman na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ado-Ekiti bisa tuhume-tuhume shida.

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

EFCC ta gurfanar da miji da mata kan damfarar kusan N2bn.
Miji da mata da EFCC ta kama kuma ta gurfanar da su kan zargin damfarar kusan N2bn. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Yadda EFCC ta kama miji da mata

Rahoton shari'ar da EFCC ta wallafa a shafinta na X ya nuna cewa tuhume tuhumen shida sun shafi damfara da boye kudaden da ake zargin an samu ta haramtacciyar hanya.

EFCC ta sanar da cewa ta kama wadanda ake zargin ne bayan wata mata mai makarantar kudi a jihar Delta, Anazia Colina Kenechukwu, ta shigar da korafi a kansu.

Matar ta bayyana cewa Taiwo ya tuntube ta yana neman ta ba shi kudin da zai yi amfani da su wajen gudanar da wata kwangilar gina hanya da ya ce hukumar DESOPADEC ta ba shi.

A cewarta, ta tura jimillar kudin da suka kai N1,980,000,000 zuwa asusun Taiwo da ke bankin Access Bank. Sai dai binciken EFCC ya gano cewa an karkatar da kudaden wajen sayen kadarori biyu a Ado-Ekiti.

Kadarorin da EFCC ta kwace

Hukumar ta bayyana cewa ma’auratan sun sayi wani wurin shakatawa mai suna Town Tavern Lounge da wani gida mai dakuna hudu da kudaden da ake zargin an samu ta damfara.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: DSS ta kai wanda ake zargi da zuga sojoji gaban kotu

An ce kadarorin suna yankin Ikere Road da Florence Court a Ado-Ekiti.

EFCC ta ce ta samu umarnin kotu a ranar 25 ga Mayu, 2026 domin karbe kadarorin na wucin gadi yayin da ake ci gaba da bincike.

EFCC ta kama miji da matar ne kan damfarar wata mata kusan N2bn
Allon sanarwa da ke wajen hedikwatar hukumar EFCC a Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Facebook

Abin da tuhumar EFCC ta kunsa

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya nuna cewa ma’auratan sun karbi N1,098,961,500 daga hannun matar ta hanyar karya cewa za a yi amfani da kudin wajen gudanar da kwangilar gina hanya.

Ana zarginsu da aikata laifin da ya saba wa dokar damfara ta AFFOFRO ta shekarar 2006, kuma ma'auratan sun musanta aikata dukkan tuhume-tuhumen a lokacin da aka karanta musu a kotu.

Lauyan EFCC, Sesan Ola, ya roki kotu ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin.

Mai shari’a Abubakar Usman ya dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis, 11 ga Yunin 2026, kuma ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ma’auratan a hannun EFCC har zuwa ranar da za a sake zama.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

Karanta rahoton a kasa:

Kotu ta garkame malami da matarsa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Mai shari'a Adeola Olatubosun ta kotun majistare dake Sabo-Yaba, jihar Legas ta tura wani malamin addini da matarsa magarkamar Ikoyi.

Ana zargin Fasto Azuka Ohez da matarsa, Mary Ohez da zambar kudade da yawansu ya kai naira miliyan 33.8 mallakin wani kamfanin mai.

An rahoto cewa ma'auratan sun hada kai da wasu mutane da suka tsere wajen karbar kaso daga kudaden da aka samu ta hanyar damfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com