An rufe duka Majalisun Tarayya na makonni 2 saboda cutar Coronavirus
A halin yanzu an rufe majalisar wakilan tarayya da kuma ta dattawa a Najeriya, a sakamakon cutar Coronavirus da ta shigo Najeriya, har ta yi sanadiyyar mutuwar wani.
A Ranar 25 ga Watan Maris, Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an rufe majalisun tarayyar domin a hana yaduwar cutar COVID-19 da ta shiga kasashe fiye da 190.
Shugaban majalisar dattawa watau Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya bada wannan sanarwa bayan wani zama da su ka yi na kusan sa’a guda a Ranar Talatar nan da ta gabata.
Ahmad Lawan ya ce Sanatoci sun dakatar da aiki a majalisar, sai dai a cewarsa, za su tsaya jiran aikin ko-ta-kwana a Abuja, su dawo bakin aiki idan akwai bukatar gaggawa.
Lawan ya ce Sanatocin za su tafi hutun makonni biyu, za su dawo bakin aiki a Ranar 7 ga Watan Afrilu. Lawan ya yi kira ga gwamnati ta dage wajen yakar wannan cuta.
KU KARANTA: Shugaban kasa ya koma bakin aiki a Aso Villa, COS ya na asibiti
A majalisar wakilai ma an dauki irin wannan mataki bayan Kakakin majalisa Femi Gbajabiamila da wasu ‘Yan majalisa takwas sun kawo wannan shawara sa'ilin zaman karshe.
An yanke wannan shawara ne jim kadan bayan majalisar wakilan ta amince da wani kudirin bunkasa tattalin kudi. ‘Yan majalisar sun kuma yi irin na su kira ga gwamnati.
Daga cikin shawarwarin da majalisar wakilai ta ba gwamnatin tarayya shi ne dakatar da karbar haraji a wannan lokaci domin ragewa jama’a radadin wannan cuta da ta shigo.
Majalisar ta tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da wannan cuta, kuma ta karyata cewa wasu su na kaurcewa binciken cutar COVID-19 da ake yi a filin saukar jiragen sama.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng