Shuwagabannin Najeriya na bukatar addu’o’in yan Najeriya domin yin aiki tukuru

Shuwagabannin Najeriya na bukatar addu’o’in yan Najeriya domin yin aiki tukuru

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai bukatar yan Najeriya su dage wajen gudanar da addu’o’i ga shuwagabanninsu domin shuwagabannin su samu daman yi musu aiki yadda ya kamata.

Lawan ya bayyana haka ne a ranar litinin yayin da yake jawabi a taron binne marigayi, tsohon Sanatan Filato ta kudu, Sanata Ignatius Longjan wanda ya mutu a watan Feburairu yana dan shekara 75.

KU KARANTA: Rikicin cikin gida: Sabon shugaban ISWAP ya halaka manyan kwamandoji 5

Shuwagabannin Najeriya na bukatar addu’o’in yan Najeriya domin yin aiki tukuru

Shuwagabannin Najeriya na bukatar addu’o’in yan Najeriya domin yin aiki tukuru
Source: Twitter

TheCables ta ruwaito a yayin jawabinsa, Lawan ya ce: “Muna bukatar kasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da tsaro. Muna bukatar addu’a matsayinmu na kasa da jama’a, nan ne ya fi dacewa mu rokeku wannan.”

Mai magana da yawun Ahmad Lawan, Ezrel Tabiowo ya bayyana cewa Sanatan ya ce addua ka iya sauya abubuwa da dama, addu’a na iya sa shuwagabanni su yi aiki, don haka shuwagabannin Najeriya na bukatar addua don su mayar da hankulansu ga shugabanci tare da samar da kasar da kowa zai yi alfahari da shi.

Daga karshe Sanatan ya bayyana marigayi Longjan a matsayin mutumin kirki dake zaman lafiya da kowa, tare da son ganin an samar da zaman lafiya musamman a jahar Filato da ma kasa gaba daya.

A wani labarin kuma, mataimakin gwamnan jahar Kogi, Edward Onoja ya koma makaranta don samun digiri na biyu da digirin digirgiir fannin zaman lafiya da warware rikice rikice a jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Lokoja.

Onoja ya bayyana haka ne a shafukansa na dandalin sadarwar zamani, inda yace a ranar Litinin ya fara daukan darasi, ya kara da cewa makasudin komawarsa makaranta shi ne don a yanzu duniya na bukatar kwararru wajen kashe wutar rikice rikice.

Mista Onoja ya kara da cewa yana fatan zai kammala karatun digirin digirgir zuwa shekarar 2023. “Na koma makaranta don karatun digiri na biyu, a bangaren zaman lafiya da warware rikice rikice na zangon karatu na shekarar 2020, inda nake sa ran samun digiri na uku a shekarar 2023.” Inji Onoja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel