ADC Ta Gamu da Koma Baya a Katsina, Masu Neman Takara 34 Sun Fice zuwa DP
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta rasa wasu mambobinta da suka nemi takara a inuwarta zuwa PDP a jihar Katsina
- Mutanen wadanda suka nemi takarar kujerun majalisar dokokin jihar sun yi korafin cewa an yi masu rashin adalci a jam'iyyar
- Shugaban jam'iyyar PDP na reshen jihar Katsina, ya yi masu maraba inda ya ba su tabbacin cewa za a yi masu adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Aƙalla mutane 34 masu neman takarar kujerar majalisar dokoki ta jiha a Jihar Katsina ne suka sauya sheka daga jam'iyyar ADC zuwa PDP.
Masu neman takarar sun bayyana rashin adalci, raunin jagoranci, da rashin samun dama a cikin ADC a matsayin dalilansu na komawa babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Source: Twitter
Jaridar Thisday ta ce an karɓi masu sauya shekar, tare da wasu daga cikin magoya bayansu daga ƙaramomin hukumomi 18 na jihar, a hukumance zuwa cikin PDP a wani taron da aka gudanar a yammacin ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026 a Katsina.

Kara karanta wannan
Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Kaduna, an kashe manyan jagorori 4
'Yan ADC sun koma PDP a Katsina
Yayin da yake jawabi a madadin masu sauya shekar, Hon. Ahmad Yusuf Jaguma ya ce shi da sauran masu neman takara 33 sun yanke shawarar barin ADC ne bayan sun cire rai da abin da ya siffanta da rashin adalci da kuma raunin jagoranci a jam'iyyar.
"Mun yi tunani mai zurfi kuma mun gano cewa PDP ce mafita. Mun watsar da tafiya maras tsari kuma mun koma asalin gidanmu.”
- Hon. Ahmad Yusuf Juguma
Meyasa suka bar jam'iyyar ADC?
Ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu sun fara shiga ADC ne da sa burin cewa jagoran siyasa na PDP a jihar Katsina, Sanata Yakubu Lado, shi ma zai sauya sheka zuwa jam'iyyar, jaridar Premium Times ta kawo rahoton.
Sai dai, ya ce lokacin da babban jigon na PDP ya gaza shiga ADC, sai suka yanke shawarar sake komawa PDP.
Yayin da yake karɓar masu sauya shekar, shugaban PDP na jihar Katsina, Hon. Nuraddeen Amadi Kurfi, ya bayyana dawowar tasu a matsayin ƙarin shaida na cewa PDP ta kasance gidan siyasa ga waɗanda ke neman adalci da daidaito.

Kara karanta wannan
'Yan APC sun tayar da hayaniya a Legas, an yi zanga zanga kan zaben fitar da gwani
Ya jaddada cewa babu wani mamba da ya bar PDP bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar, inda ya danganta hakan da yanayi na haɗin kai da kuma dimokuraɗiyya ta cikin gida da ke wanzuwa a jam'iyyar.
PDP za ta ba masu son takarar dama?
“Za ku samu cikakkiyar dama da adalci a PDP. Wannan jam'iyya gida ce ga kowa, kuma muna da yakinin cewa za ku yi alfahari da shawarar da kuka yanke."
- Hon Nuraddeen Amadi Kurfi
Yayin da yake jawabi ga masu sauya shekar, ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2027, Sanata Yakubu Lado, ya tabbatar wa sababbin mambobin cewa za a yi musu adalci daidai da kowa.

Source: Facebook
Yakubu Lado ya sake jaddada cewa ƙofofin jam'iyyar a buɗe suke ga duk wanda ya fuskanci tsangwama ko rashin adalci a wani wurin.
Ya nuna kwarin gwiwar cewa ƙarin 'yan siyasa za su biyo baya nan ba da jimawa ba don shiga PDP, ya bayyana cewa tuni jam'iyyar take tattaunawa da manyan jiga-jigan siyasa da dama a faɗin jihar.
Nasiru Gawuna na shirin komawa ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a inuwar NDC a zaben 2027, Nasiru Yusuf Gawuna, na duba yiwuwar sauya sheka zuwa ADC.
Shugaban ADC na Kano, Musa Ungogo ya ce Gawuna ne ya fara tattaunawar ta hanyar wasu wakilai waɗanda suka haɗu da shugabannin jam'iyyar.
Musa Ungogo ya bayyana cewa cikin buƙatun da ɓangaren Gawuna ya gabatar har da tikitin takarar gwamna na ADC don zaɓen shekarar 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
