Duk da tarin bashin N33tr Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta cikin matsala

Duk da tarin bashin N33tr Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta cikin matsala

Majalisar dattawa ta yi magana game da aron kudin da gwamnatin Najeriya ta ke yi. Hakan na zuwa ne bayan an amincewa gwamnatin tarayya karbo bashin Dala biliyan 22.7.

A sakamakon amincewar da aka yi wa gwamnatin tarayya na karbo aron wasu makudan kudin, yanzu bashin da ke kan wuyan Najeriya ya kai Naira tiriliyan 33 inji hukumomi.

Sanata Muhammad Enagi Bima wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin bashi da aron kudi a majalisar dattawa ya bayyana wannan a wajen wata lacca da NILDS ta shirya.

Muhammad Enagi Bima mai wakiltar Jihar Neja ya bayyana cewa amfani da kudin bashi wajen kawowa kasa cigaba ya zamewa kasashe masu tasowa irin Najeriya ciwon-kai

Bima ya ke cewa idan aka duba irin kudin da Najeriya ta aro daga 2006 zuwa yanzu, kuma aka yi la’akari da abubuwan more rayuwar da ke kasar, za a ga cewa an yi hannun riga.

KU KARANTA: An roki Majalisa ta hana Buhari karbowa Najeriya bashin $22b

Duk da tarin bashin N33tr Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta cikin matsala
Majalisar dattawa ta ba Buhari damar karbo wasu danyen bashi a ketare
Source: UGC

Sanata Enagi Bima yace bashin gida da na kasar wajen da ke kan gwamnatin Najeriya yanzu kamar yadda hukumar DMO ta bayyana ya kai Naira tiriliyan 26.2 (Dala biliyan 85.4.)

Bankunan gida su na bin gwamnatin tarayya bashin Naira tiriliytan 11. Bayan amincewa da sabon rokon bashin gwamnatin kasar, kudin da ake bin kasar ya koma Naira tiriliyan 33.

Sanatan ya nuna dole a bi a hankali game da irin kudin da gwamnati ta ke arowa. A cewarsa ya kamata a rika yi wa kasa ayyuka ne da wannan kudi ba kawai a tula mata bashi ba.

A na ta jawabin, shugabar hukumar DMO mai kula da bashin Najeriya, Misis Patience Oniha, ta nuna tsoron cewa cutar coronavirus na iya hana Najeriya biyan bashin da ke kanta.

Patience Oniha ta ce hankalin jama’a ya na tashi saboda ganin yadda gwamnati ta komawa cin bashi bayan 2005. Sai dai duk da haka ta ce lamarin bai kai a tada hankali ba tukuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel