Yadda Yan Bindiga Suka Harbe Wani Dattijo bayan Sace Mutum 39 a Zamfara

Yadda Yan Bindiga Suka Harbe Wani Dattijo bayan Sace Mutum 39 a Zamfara

  • Daya daga cikin dattawan da aka sace a Zamfara ya rasu a hannun ‘yan bindiga yayin da ake tsare da su bayan miyagun mutanen sun yaudare su
  • Wani dattijo mai suna Ali Zagaru da ya tsere daga cikin sansanin ‘yan bindigan tare da bayyana halin azabar da suka fuskanta a hannun mutanen
  • ‘Yan bindigan sun sanar da kudin da suke bukata a biya su matukar ana son su sako sauran mutanen da suka yi garkuwa da su daga zaman sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Wani daga cikin dattawan kauyuka 39 da aka yi garkuwa da su a wani yunkurin zaman sulhu da bai yi nasara ba a cikin dajin Zamfara ya mutu a hannun masu garkuwa da mutanen.

Kara karanta wannan

Dalibai sun fara gudun neman tsira da wani malami ya yi shigar 'yan bindiga a makaranta

Rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin wadanda aka sace ya samu nasarar tserewa daga sansanin ‘yan bindigan.

An hallaka daya daga cikin dattawan Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalar yan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton da ya kebanta ga jaridar Leadership ya bayyana cewa Ali Zagaru, wanda ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen a daren Talata, 9 ga watan Yuni, 2026.

Dattijo a Zamfara ya rasu wurin 'yan bindiga

Ali Zagaru ya bayyana cewa marigayi Bako Abdullahi Yarfara mai shekaru 67 ya rasa ransa ne bayan ya kasa tafiya da saurin da ‘yan bindigar suke bukata yayin da suke kai su cikin zurfin daji.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Yuni, 2026 ranar da aka sace su tare da sauran dattawan yankin daga zaman sulhu.

Ya ce bayan harbin marigayin, ‘yan bindigan sun kai gawarsa wani kauye da ke kusa inda aka yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

'Yan bindiga sun nemi kudin fansa

Ali Zagaru ya ce shugaban ‘yan bindigan da aka fi sani da Jammo ya nemi al’ummar Magamin Diddi su biya Naira miliyan 125.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 6 sun mutu yayin da suka yi yunkurin kai hari a jihar Zamfara

Ya bayyana cewa daga cikin kudin, Naira miliyan 25 na da alaka da bindigu kirar AK-45 guda biyu da jami’an tsaro suka kwato bayan kashe wasu daga cikin mutanensa.

Sai kuma sauran Naira miliyan 100 kudin fansa ne domin a sako dattawan tare da ba wa al’ummar yankin damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.

Yan ta'adda sun nemi fansa daga hannun yan ta'adda
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ali ya ce rayuwa a sansanin ‘yan bindigar akwai azaba. Ya bayyana cewa ana muzgunawa wadanda aka sace a kullum, yayin da abincin da suke samu ya yi karanci sosai tun bayan kama su.

Ya kara da cewa ya samu damar tserewa ne bayan ya bi wata boyayyar hanya ba tare da masu gadin sansanin sun lura da shi ba.

An sace dattawa a jihar Zamfara

A baya, mun kawo labarin cewa wasu dattawa daga kauyen Magamin Diddi sun fada hannun ‘yan bindiga yayin wata tafiyar sulhu don tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani shugaban dabar ‘yan bindiga da ake kira Jammo ne ya yi garkuwa da su a dajin Muntsira bayan an yaudare su da maganar sulhu.

Haka zalika, bayanai sun nuna cewa an sako mutum 11 daga ciki, yayin da har yanzu mutum 39 ke hannun masu garkuwa da mutanen inda ake ci gaba da zaman fargaba kan halin da suke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng