Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattijai da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)

Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattijai da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)

A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Su biyun sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a fadarsa da ke Abuja, babban birnin tarayya kasar nan, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya wallafa.

Duk da har yanzu babu cikakken bayani a kan taron, za a iya danganta shi da rashin tsaron da yayi kamari a yankin Arewa maso gabas din kasar nan.

Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Asali: Twitter

Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Asali: Twitter

Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattija da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)
Asali: Twitter

A wani labari na daban kuma, mun ji cewa Gwamnan jihar Bayelsa, Diri Douye a ranar Talata ya ce ya kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara ne domin ya gabatar da kan shi ga shugaban kasar a hukumance.

Douye ya yi bayanin cewa tun lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna a ranar 14 ga watan Fabrairun 2020 jiya (Talata) ce karo na farko da ya ziyarci shugaban kasar a fadarsa ra Aso Villa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Bayan kammala taronsa da shugaban kasa misalin karfe 1.39 na rana, ya shaidawa manema labarai na gidan gwamnati cewa a shirye ya ke ya yi aiki tare da gwamnatin tarayya domin tabbatar da zaman lafiya a jiharsa.

Idan ba a manta ba Duoye ya zama gwamnan Bayelsa ne bayan hukuncin kotun koli na kasa a ranar 13 ga watan Fabrairun 2020 da aka soke zababbun 'yan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mista David Lyon da mataimakinsa awanni 24 kafin a ranstar da shi.

Gwamnan ya ce, "Tunda na fara aiki a matsayin gwamnan jihar Bayelsa, ban zo na gaishe da uban kasa ba. A yau, gashi na aikata hakan; na zo na ziyarci uban kasar mu kuma domin muyi aiki tare da gwamnatin tarayya domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa a jiha ta. Wannan shine dalilin da yasa na ziyarci shugaban kasa a yau."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel