Dalibai Mata Sun Diro daga Bene da Wasu Miyagu Suka Kai Hari Kwalejin Lafiya a Najeriya
- Wasu miyagu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari dakin kwanan dalibai mata a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Ngbo, jihar Ebonyi
- Rahotannni sun nuna cewa dalibai mata tara sun samu raunuka yayin da suke kokarin tserewa daga saman bene
- Mahukunta sun ce babu wani dalibi da ya bace bayan harin, kuma ana zargin wasu na cikin makarantar sun taimaka wa maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi, Nigeria - Akalla dalibai tara ne suka jikkata bayan wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari dakin kwanan dalibai mata na Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha, Ngbo da ke karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi.
Shugabar kwalejin, Gimbiya Chetachi Usulor, ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:20 na dare a ranar 9 ga watan Yunin 2026.

Source: Original
Mahara sun shiga dakunan dalibab kwaleji
A rahoton Channels tv, Gimbiya Chetachi ta ce maharan sun shiga dakin kwanan daliban tare da fara kwace wayoyin hannu, kudi, katunan ATM da sauran kayayyaki masu daraja daga hannun daliban.
Ta ce bayan ta samu labarin abin da ke faruwa, nan take ta tuntubi jami'an tsaro domin neman dauki.
"Na kira layin gaggawa na 'yan sanda, ofishin 'yan sanda na yankin da kuma jami'an tsaron cikin gida. Da mutane suka fara zuwa wurin, sai maharan suka tsere," in ji ta.
Dalibai 9 sun jikkata yayin tserewa
Shugabar kwalejin ta bayyana cewa daliban da suka samu raunuka ba maharan ne suka kai musu hari kai tsaye ba.
Ta ce wasu daga cikin daliban da ke zaune a saman bene sun yi tsalle suka diro ta tagogi saboda tsoro da kokarin boye wayoyinsu daga hannun maharan.
Gimbiya Chetachi ta ce:
"Wasu daliban da ke saman bene sun diro ta tagogi saboda tsoro. Raunukan da suka samu sun samo asali ne daga fadowar da suka yi."
Ta kara da cewa an garzaya da daliban asibiti domin yi musu gwaje-gwaje kamar hoton X-ray da sauran binciken lafiya. A cewarta, dalibai tara ne ke karbar magani a halin yanzu.

Source: Facebook
Da gaske wasu dalibai sun bace?
Usulor ta karyata rahotannin da ke cewa wasu dalibai sun bace bayan harin, inda ta jaddada cewa an kirga dukkan daliban kuma babu wanda ya bata.
Shugabar kwalejin ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin mutanen makarantar sun taimaka wa maharan, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ta ce rahotanni sun nuna cewa wata mace na cikin mutanen da suka kai harin, inda ake zarginta da nuna wa maharan dakunan da za su shiga su yi sata.
'Yan bindiga sun shiga makaranta a Kogi
An ji cewa 'yan bindiga sun kai mummunan hari makarantar sakandaren gwamnati da ke Iluke Bunu a karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun yi sanadin mutuwar mutum uku, ciki har da Mataimakin Shugaban Makaranta, Malam Gani Anifowose.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa manufar maharan ita ce kai hari kan daliban da ke rubuta jarrabawar WAEC a makarantar.
Asali: Legit.ng


