Rashin Tsaro: An Kai Dattawan Arewa Wuya, Sun Kawo Mafita ga Shugaba Tinubu
- Kungiyar dattawan Arewa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi gaggawar kawo karshen matsalar tsaro a kasar
- Dattawan sun bukaci ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro, tana cewa Najeriya na fuskantar mummunar barazana
- NEF ta ce sace-sacen mutane, ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga sun mamaye yankuna da dama, lamarin da ya jefa al'umma cikin tsoro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Yayin da matsalolin tsaro ke kara kamari a Najeriya, Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta ba Bola Ahmed Tinubu shawara.
Ƙungiyar dattawan ta bukaci Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma kamar yadda ya yi alƙawari.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa Abubakar Jiddere ya sanya wa hannu, cewar Punch.
Matakan da ake buƙata kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan
Alwashin sojojin Najeriya, Amurka kan tsaro bayan hare hare sun karu a Kudu da Arewa
Manyan na Arewa sun ce matsalar tsaro ta kai matsayin da ke bukatar daukar matakai na gaggawa.
Ta ce idan ba a dauki tsauraran matakai ba, akwai yiwuwar kasar ta fada cikin rudani da rashin doka da oda.
Kungiyar ta bayyana cewa 'yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro, al'ummomi na fuskantar hare-hare, yayin da masu aikata laifuka ke kara samun karfin guiwa.
Sanarwar ta ce:
"Kungiyar Dattawan Arewa ta nuna matukar damuwa kan yadda tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a fadin Tarayyar Najeriya."
Ta kara da cewa babu wata kasa da za ta yi ikirarin ci gaba idan mutanenta na rayuwa cikin tsoro, yayin da miliyoyin masu bin doka suke cikin hadari.

Source: UGC
Jihohin da hare-hare suka zama ruwan dare
Kungiyar ta tambayi dalilin da ya sa 'yan kasa ke kare kansu daga masu garkuwa, 'yan ta'adda da kungiyoyin masu aikata manyan laifuffuka.
Ta ce tun bayan samun 'yancin kai a 1960, Najeriya ta fuskanci kalubalen tsaro iri-iri, amma ba a taba ganin irin wannan ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
"Ku yi murabus cikin mutunci," Majalisar wakilai ta ba hafsoshin tsaron Najeriya zabi 2
A cewarta, daga Zamfara da Katsina zuwa Kaduna da Neja, daga Plateau da Benue zuwa Kogi, Kwara, Borno, Oyo, Edo, Enugu da Imo, hare-hare sun zama ruwan dare.
Kungiyar ta ce ana kai wa al'ummomi farmaki, ana sace mutane, manoma suna barin gonakinsu, yayin da matafiya ke fuskantar hari a manyan hanyoyi.
Ta bayyana cewa rahotannin tsaro masu zaman kansu sun nuna dubban mutane sun mutu ko an sace su sakamakon ayyukan miyagu.
NEF ta ce matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta rikide zuwa wata babbar kasuwanci ta ta'addanci mai cin gajiyar raunin tsaro.
Dattawan Arewa sun soki Tinubu, Atiku, Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF, ta bayyana damuwa game da salon mulkin Bola Tinubu bayan zaɓen 2023.
Kungiyar ta ce Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su gabatar da sahihin tsarin da zai gamsar da yankin Arewa ba.
Ta bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da talauci za su yi tasiri a zaɓen 2027 da ake tunkara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng