Abun Al Ajabi
Cibiyar nazarin harkokin bincike da bunkasar kasa ta NASRDA (National Space Research and Development Agency) ta bayyana wasu jihohi hudu na kasar nan gami da babban birnin tarayya na Abuja da girgizar kasa ka iya aukuwa cikinsu.
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta cafke wasu miyagun 'yan ta'adda 15 da suka shahara da garkuwa da mutane, satar dabbobi da kuma fashi da makami.
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, wata matashiyar uwargida mai shekaru 20 a duniya, Zulac Kabiru, ta amsa laifinta na sheke jaririyar kishiyar ta har lahiya 'yar watanni takwas da haihuwa, Rukaiya Kabiru.
Za ku ji cewa 'yan uwan wani dalibi, Damilare Taiwo, sun shiga cikin hali na matsananciyar damuwa yayin da suka samu rahoton mutuwar sa bayan kwana guda da shiga makarantar horas da dakurun soji dake jihar Kaduna.
Wannan Mata mai suna Angie Jewitt ta bayyana cewa fatan shine Allah ya raya wannan tinkiya a yadda aka halicceta, don haka ne ma ta wareta daga cikin sauran tumakanta domin ta bada kyakkyawar kulawar da take bukata.
Mun samu cewa wata Kotun Majistire dake zamanta a garin Ebute Meta na jihar Legas, ta bayar da umarnin garkame wani matashi mai shekaru 25 a gidan kaso, Taiwo Akinola, bisa aikata laifin halin dan yau da ya sheme Mahaifiyarsa.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da tabbacin salwantar rayukan wani soja da kuma wasu Mutane 9 sakamakon aukuwa 2 ta ambaliyar a yankuna daban-daban dake jihar.
Mun samu cewa hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta yi wata gagarumar nasara ta cafke wasu miyagun 'yan ta'adda da suka shahara da kashe-kashe, garkuwa da mutane, kwacen motoci gami da fashi da makami a wasu birane da kauyukan Arewa.
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, a watan Okotoba mai gabatowa hukumar 'yan sanda ta Najeriya za ta kaddamar da wata sabuwar manhaja ta cafke barayin motoci tare da cafke duk wata mota da aka sata a kasar nan.
Abun Al Ajabi
Samu kari