Yadda ’ya’yana maza 3 suka makance suna samari – Inji wata uwa

Yadda ’ya’yana maza 3 suka makance suna samari – Inji wata uwa

Allah sarki duniya, kowani mutum da irin ibtila’in da Allah ke jarabtar shi dashi, a cikin haka wasu kan karbi nsu jarabawar hannu bibbiyu yayinda kuma sai ku ga wasu sun kauce hanya.

Hakan ce ta kasance da wata mata mai suna Hajiya Huraira Muhammad wacce ke da zama a bayan babban masallacin Lafiya, babbar birnin jihar Nasarawa.

Hajiya Huraira ta bayyana yadda yaranta maza har su uku suka makance daya bayan daya, inda sauran yaran nata mata su uku kenan garau da idanunsu.

Matar ta mika godiya ga Allah inda ta bayyana cewa duk da wannan lalurar da ya samu yaran nata basa bara, harma tace sun fi wasu masu idanun kokarin neman na kansu.

A wata hira da matar tayi da jaridar Aminiya a garin Lafiya, ta ce, “Allah Ya ba ni haihuwa shida, uku maza sannan kuma uku mata. Amma abin mamaki shi ne, mazan uku duk sun makance.

“Babban dana ya yi zazzabi, aka yi masa karin ruwa, bayan kwana uku, sai na ce ya fito waje don ya sha iska, sai ya ce ba ya gani sosai. Sai muka sa aka yi rokon Allah Ya samu sauki, daga bisani dangi suka yi taron gaggawa, aka kai shi asibiti a Kano, suka tambaye mu ko mun kai shi aikin walda ne ko ciwon gadon gidanmu ne, muka ce a’a, babu ko daya. Bayan gwaje-gwaje, sai suka ce mu koma gida mu hakura.”

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar yan shi’a: Majalisar dattawa ta dauki mataki, ta tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar

Ta ci gaba da cewa: “Bayan nan sai na biyu ya kamu da irin ciwon, kuma sai shi ma na ukun ya kamu. Amma na gode wa Allah domin duk da cewa mahaifinsu ya rasu, ba sa yin bara, har sun fi wadansu masu idon kokarin neman na kansu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel