Babban Sarki a Najeriya ya bukaci Ingila ta dawo da kayan tarihin masarautar sa

Babban Sarki a Najeriya ya bukaci Ingila ta dawo da kayan tarihin masarautar sa

Sarkin Benin, Ewuare II, ya bukaci yariman kasar Wales, Charles George, da ke ziyara a Najeriya, da ya saka baki domin ganin kasar Ingila ta dawowa da masarautar sa kayan tarihin da ta kwasa a shekarar 1857.

Sarkin ya bayyana cewar dawo ma sa da kayan tarihin zai bashi damar gina gidan tarihi da zai bunkasa tarihi da yawon bude ido a birnin Benin, jihar Edo.

Ewure II na wadannan kalamai ne a cikin wani jawabi da ya gabatar yayin ganawa da yarima mai jiran gadon sarautar kasar Ingila a wani taro da su ka yi jiya a gidan jakadancin kasar Ingila da ke unguwar Maitama a Abuja.

Ragowar sarakunan gargajiya da su ka halarci taron sun hada da Sarkin kasar Ife, Enitan Ogunwusi; Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar; Sarkin Onitsha, Igwe Alfred; Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da sauran su.

Babban Sarki a Najeriya ya bukaci Ingila ta dawo da kayan tarihin masarautar sa
Prince Charles da sarakunan Najeriya
Asali: UGC

Yarima Charles, ya ziyarci shugaba Buhari kafin ganawa da sarakunan na gargajiya a cigaba da ziyarar kasashen Afrika da su ka hada da Gambia, Ghana, da Najeriya.

Sarkin na Benin ya yi waiwaye a kan kyakykyawar dangantakar da ke tsakanin masarautar sa da ta kasar Ingila tare da bayyana irin zumunci da fahimtar juna da ke tsakanin su.

DUBA WANNAN: An bawa Hadiza Gabon kyautar dankareriyar mota, hoto

Sarkin ya shaidawa manema labarai cewar sun tattauna a kan batutuwan da su ka shafi tsaro, matsalar safarar mutane da kuma ilimin 'ya'ya mata.

Kazalika, Sarkin Kano ya ce sun tattauna a kan matsalolin da su ka shafi yanayi da muhalli, yadda za a shawo kan yawon jama'a da matsalar da za a iya fuskanta idan ba a yi hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel