Mutuwar Uwa, Fadan ‘Ya ‘yansa da Abubuwa 10 da Suka Faru da El Rufai da Yake Tsare
Abuja - Abubuwa na farin ciki da na bakin ciki sun faru da Nasir El-Rufai a halin yanzu da yake tsare a hannun hukuma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Tun a watan Fubrairun 2026 jami’ai suka yi ram da shi jim kadan bayan ya dawo Najeriya inda hukumomi suke binciken shi.
Manyan abubuwan da suka faru da shi sun hada rasa mahaifiyarsa, shari'o'i a kotu zuwa cigaban da ake samu a jam’iyyar ADC.

Source: Facebook
Abubuwan da suka faru da Nasir El-Rufai
Mun yi kokarin tattaro abubuwa marasa dadi da suka faru da tsohon gwamnan na Kaduna a watanni kusan 10 da suka wuce.
1. Kin bada belin Nasir El-Rufai
A Oktoban nan aka ji cewa Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke na ba Nasir El-Rufai beli kamar yadda ya nema.
Lauyoyinsa sun fada wa kotu cewa tsare shi da ake ta yi ya hana tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya iya kare kan shi daga tuhumomi.
2. Rashin nasara a shari’arsa da AGF, dsr
An shafe wata da watanni ana rike da ‘dan siyasar, amma bayan haka ya yi rashin nasara a karar da ya kai ICPC, DSS, AGF da sauransu.
A makon nan aka ci Malam tarar kudi da zai biya hukumomin da ya ke kalubalantar su biya shi N120m saboda sun nemi cafke shi a filin jirgi.
3. Matsalar rashin lafiya
Iyalin Malam El-Rufai sun koka cewa yana fama da matsalar ido kuma ana zargin ya kamu da cutar daji don haka ake so ya ga likita.
Alkali bai gamsu da wannan magana ba kuma ya ki bada belin shi da nufin ya ga likita saboda asibiti ya karyata rahoton da aka bada.
4. Cafke likitan El-Rufai
A sanadiyyar rahoton rashin lafiyan da aka ba kotu, likitan ‘dan siyasar ya shiga matsala har ana zargin sa da yi wa hukuma karya.
An rahoto cewa hukumar ICPC ta cafke Farfesa Bello Abubakar wanda shi ne babban likitan da yake kula da lafiyar Malam El-Rufai.
5. Hana iyali ganin shi
Baya ga korafin hana shi ganin likita, akwai zargin cewa hukumomi sun ki bari iyali da ‘yanuwa da sauran jama’a su ga El-Rufai.
A Agusta aka ji mai dakinsa, Aichatou Djibril Asabe ta na cewa jami’an ICPC sun hana ta ganin mai gidansu da ta je kai masa abinci.
6. Korar jami’in ICPC daga aiki
Ba likitan tsohon ministan na Abuja kadai ya shiga matsala ba, akwai wani ma’aikaci da aka sallama daga ICPC saboda wannan lamari.
The Cable ta rahoto cewa hukumar ICPC ta fatattaki jami’in daga aiki saboda ya kyale matar El-Rufai ta gan shi ba tare da izini ba.
7. Zanga-zanga da kukan matarsa
Wata matar tsohon gwamnan, Asiya Ahmad ta kira taron manema labarai a kwanakin baya domin shaida wa duniya halin da suke ciki.
Lauyar kuma marubuciya ta bukaci mahukunta su yi wa mijin nasu adalci, a gurfanar da shi a kotu ba kawai a cigaba da garkame shi ba.
8. Matsala a jam’iyyar ADC
‘Yan bangaren El-Rufai ba su ji dadin abin da ya faru zaben tsaida gwanin ‘dan takaran gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar ADC ba.
Saboda an ba Isa Ashiru Kudan takara ne mutanensa irinsu Bashir Sa’idu, Jafar Sani da Sulaiman Kwari suka koma wajen Uba Sani a APC.
9. Rigimar ‘ya ‘yan El-Rufai
A sa’ilin da Nasir El-Rufai yake tsare sai aka ga ‘dansa mai suna Bashir El-Rufai ya fito dandalin X yana kaca-kaca da ‘danuwansa, Bello.
Bashir El-Rufai wanda ya saba jawo abin magana ya jefi ‘dan majalisar da zargi masu karfi. A yanzu babu duriyarsa a dandalin sada zumunta.
10. Mutuwar mahaifiyarsa
Babban abin da zai yi wa El-Rufai ciwo shi ne mahaifiyarsa da ta cika a Maris, amma abin farin cikin shi ne an kyale shi ya je jana’iza da makoki.
Bayan an gama zaman makoki an cigaba da tsare jagoran na ADC. Yayansa Bashir El-Rufai bai iya zuwa Najeriya duk da rasa tsohuwarsu ba.
Nasir El-Rufai ya shiga kwamitin yakin zabe
An ji cewa Atiku Abubakar ya naɗa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin kamfen na jam'iyyar ADC.
An yi naɗin ne duk da cewa El-Rufai na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun hukumar ICPC bayan kama shi da aka yi a farkon shekarar nan.
Kwamitin wanda su Kashim Ibrahim-Imam zai jagoranta ya kunshi gogaggun ƴan siyasa irinsu Sanata Aminu Tambuwal domin tunkarar zaben 2027.
Asali: Legit.ng



