An gano wani gari da aka shafe shekaru 10 ba a haifi namiji ba

An gano wani gari da aka shafe shekaru 10 ba a haifi namiji ba

An gano wani gari mai sunan Miejsce Odrzanskie a Kudancin kasar Poland wanda mutanensa suka shafe shekaru goma ba tare da haihuwar da namiji ba a cikin sa.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, magajin garin Rajmund Frischko, ya yi alkawarin cewa duk ma'auratan da suka rabauta da haihuwar da namiji za su samu gagarumar kyauta da basu taba tsammani ba.

Baya ga wannan gagarumar kyauta, Frischko ya ce za a sanyawa daya daga cikin bishiyoyin garin sunan dan da aka haifa.

Shi dai wannan gari da bai sharaha ba koda kuwa a kasar ta Poland ballantana kuma a duniya, yana da yawan gidaje da ba su wuce guda 100 ba. Ya na kuma da arzikin gandu da kuma ciyayi masu yawan gaske gwanin sha'awa.

Legit.ng ta fahimci cewa, yawaitar mata da kuma karancin maza a garin na Miejsce Odrzanskie na ciwa al'ummarsa tuwo a kwarya.

Damuwar al'ummar garin ta bayyana a yayin da 'yan mata suka fito kwansu da kwarkwata wajen neman su koyi aikin kwana-kwana musamman kashe wutar gobara. Wannan lamari ya ja hankalin 'yan jarida da masu binciken kwa-kwaf.

KARANTA KUMA: Kisan 'yan Najeriya: Buhari zai gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu

Batun haihuwa dai a nahiyyar Turai na ci gaba da fuskantar tasgaro musamman yadda ma'aurata su kan zabi haihuwar da guda kacal ko kuma biyu in sun yi yawa uku.

Baya ga wannan lamari da ke haddasa karancin haihuwa, auren jinsi ya samu karbuwa inda namiji ke iya dan uwansa namiji haka kuma mace na iya auren 'yan uwarta mace da ya zamto al'ada a nahiyyar ta Turai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel