Kuji abin al'ajabi: Wasu tagwaye sun mutu a daidai ranar da aka haifesu, kuma cikin irin yanayin da aka haifesu

Kuji abin al'ajabi: Wasu tagwaye sun mutu a daidai ranar da aka haifesu, kuma cikin irin yanayin da aka haifesu

Lallai Allah buwayi ne gagara misali, Ya kan shirya abunsa yadda ya so kuma hakan shine daidai. Wani abun al’ajabi ya faru inda wadansu tagwaye masu suna Isah Muhammad da Dauda Muhammad yan shekara 22 da ke zaune a garin Jos, babbar birnin Jihar Filato, suka yi mutuwar da jefa mutane cikin alhini da juyayi a dare ranar Litinin da ta gabata.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa tagwaye da ke zaune a Unguwar Rikkos a garin Jos, sun amsa kirtan Allah a daidai ranar da aka haife su da kuma cikin irin yanayin da aka haife su.

Yayan tagwayen, Alhaji Musa Yaro Rikkos ya yi bayanin cewa wannan rasuwa ta tagwayen ta zo da abin al’ajabi. Domin kusan yadda Allah Ya kawo su duniya haka Allah Ya karbi abinSa.

Ya ce, a lokacin da tagwayen suka zo duniya shekara 22 da suka gabata, an fara haifar Muhammad Isah ne a gida, sai haihuwar ta zo da tangarda inda aka nemo mota aka dauki mahaifiyarsu zuwa asibiti, kafin a isa asibitin, sai aka haifi na biyun Muhammad Dauda.

Ya ci gaba da cewa, a lokacin da Allah Ya tashi karbarsu wanda aka fara haifa Muhammad Isah, babu dogon rashin lafiya a ranar Litinin din sai jikinsa ya canja sai aka kira likiti don ya kara masa ruwa a gida.

Musa ya kara da cewa, an fara kara masa ruwan ke nan ba a dade ba, sai Allah Ya karbi abinsa, ya rasu da misalin karfe 8:30 na dare.

A nashi bangaren bayan sanar masa da batun mutuwar dan uwansa, Muhammad Dauda na waje tare da abokansa har zuwa 10:30, sannan ya koma ciki domin kwanciya.

Bayan shigarsa ciki ba da jimawa ba, sai wadandaa suke kwana tare suka ji numfashinsa yayi sama, don haka suka je suka sanar ma yayan nasu. Isowar yayan nasu ke da wuya aka dauke shi domin garzayawa dashi asibiti da misalin karfe 11:00 a dare, a hanyarsu ta zuwa asibitin ne yace ga garinku.

KU KARANTA KUMA: Allah daya gari banban: Garin da ake daukar kunkuru kamar gwal

Dan uwan nasu ya kara da cewa, abin alájabi tagwayen an haife su ne a ranar Litinin shekara 22 da suka gabata, kuma suka rasu a ranar Litinin a daidai lokacin da aka haife su. Sannan wanda aka haifa a gida, ya rasu a gida, dayan da aka haifa a hanyar asibiti shi ma ya rasu a kan hanyar zuwa asibiti.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel