Yan Majalisa 8 da Suka Bar APC Sun Canza Shawara bayan Haduwa da Shugaba Tinubu
- ’Yan majalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka fice daga APC makonnin baya sun gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja
- Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, ne ya jagorance su zuwa wajen shugaban ƙasar, tare da ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Sani Jaji
- ’Yan majalisar ba za su koma jam’iyyar ADC ba kamar yadda aka yi ta yaɗa rahotanni, yayin da ake ƙoƙarin magance korafe-korafensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa ’yan majalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka yi murabus daga jam’iyyar APC makonnin da suka gabata sun canza shawara.
Bayanai sun nuna cewa yan Majalisar sun gana da Shugaba Bola Tinubu a daren jiya, Lahadi, 18 ga watan Oktoba, 2026 a fadar dhugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan daba ɗauke da makamai sun kewaye jigon APC, sun kashe shi nan take

Source: Twitter
Jaridar Nigerian Affairs Journal ta tabbatar da ganawar yan Majalisar da Shugaba Tinubu da wani rahoto da ta wallafa hade da hotuna a shafinta na X.
Yan majalisa 8 sun gana da Tinubu
Rahoton ya bayyana cewa bayan ganawarsu da mai girma shugaban kasa, yan Majalir gudana takwas sun yanke shawarar komawa jam’iyyar APC domin yin aiki don samun nasararta a babban zaɓen 2027.
Karamin Ministan Tsaro na Kasa, Bello Matawalle, ne ya jagorance su zuwa wajen shugaban ƙasar, tare da ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Aminu Sani Jaji.
Duk da rahotannin da suka bayyana cewa suna shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, ’yan majalisar sun sauya tunani, sun ce ba za su koma jam’iyyar adawar ba.
An ruwaito cewa sun soke matakin da sua dauka na fita daga APC yayin da ake ɗaukar matakan magance korafe-korafensu bayan ganawar da suka yi da shugaban ƙasa Bola Tonibu.
Jerin dunayen yan majalisar
Ga sunayen ’yan majalisar takwas da mazaɓunsu:
- Hon. Aliyu Ango Kagara, mai wakiltar mazabaooo Talata Mafara ta Kudu
- Hon. Ibrahim Tukur Bakura mai wakiltar mazabar Bakura
- Hon. Faruk Musa Dosara mai wakiltar mazabar Maradun I
- Hon. Bashir Abubakar Masama mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Arewa
- Hon. Muktaru Nasiru Kaura mai wakiltar mazabar Kaura ta Arewa
- Hon. Nasiru Abdullahi mai wakiltar mazabar Maru ta Arewa
- Hon. Bashar Bello mai wakiltar mazabar Bungudu ta Yamma
- Hon. Bashar Aliyu mai wakiltar mazabar Gummi I.

Source: Twitter
Tun farko yan Majalisar sun sanar da ficewa daga APC ne bisa abin da suka kira gazawar gwamnati mai ci wajen magance matsalar tsaro da sauran kalubale.
Sai dai bayan ganawa da Tinubu, an ruwaito cewa yan Majalisar sun canza shawara sun koma APC mai mulki.
Yadda aka dakatar da yan majalisa 8
A baya, kun ji cewa Majalisar dokokin Zamfara ta ce ’yan majalisa takwas da suka sanar da ficewa daga APC an dakatar da su tun watan Fabrairun 2024.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara , Rt. Hon. Moriki ya ce an dakatar da ’yan majalisar ne bisa zargin aikata rashin da’a, hada baki, aikata barna, raina majalisa da kuma gudanar da zaman majalisa ba bisa ka’ida ba, wanda ya saba wa doka.
Asali: Legit.ng
