DSS Ta Gurfanar da Wadanda Ake Zargi da Laifin Garkuwa da ‘Yan NYSC 20

DSS Ta Gurfanar da Wadanda Ake Zargi da Laifin Garkuwa da ‘Yan NYSC 20

  • DSS ta kamo wasu mutanen da ta ke zargi da yin garkuwa da jama’a a kan titin Owerri zuwa Onitsha
  • Jami’an tsaro sun gurfanar da su a wata babbar kotun jihar Imo domin a fara sauraron shari’arsu
  • Zargin da ake yi masu a wasu shari’o’i biyu sun kunshi garkuwa da mutane da mallakar makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Jami’an tsaro na DSS sun gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da laifin garkuwa da bayin Allah.

Ana tuhumar wadannan mutane da laifin sace mutane 24 daga ciki har da ‘yan NYSC 20 domin samun kudin fansa.

Yan sanda
'Yan sanda sun kama wani mai zanga-zanga a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Asirin masu garkuwa da mutane yana shirin tonuwa

Rahoton da Punch ta fitar ya ce an yi karar su a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba 2026 a babban kotun jihar Imo.

DSS ta tuhumi wadanda ake kara da laifin makirci, garkuwa da mutane da kuma mallakar makami ba tare da ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare

Usman Aliyu, 25, (Chonge); Babangida Aliyu, 21; Mohammed Ali, 23 (Smallie Pepper) ake zargi da sace masu NYSC.

Ana zargin mutanen nan uku sun yi wannan ta’asa ne ranar 1 ga watan Oktoba 2026.

DSS ta yi kara a babbar kotu a jihar Imo

Takardun da aka gani sun nuna an shigar da karan ne a babban kotun jihar Imo mai zama a Oru da ke yankin Mgbidi.

Ana zargin wadanda ake kara da sace fasinjoji a hanyar Owerri-Mgbidi-Onitsha lokacin sun taso daga Ibadan, Oyo.

Wadanda aka dauke suna kan hanyoyin zuwa jihohin Abia da Akwa Ibom ne domin yi wa kasa hidima wato NYSC.

Laifuffukan da ake zargin su da aikatawa

Jaridar The Cable ta ce DSS ta zargi wadanda aka gurfanar da shirya makirci, dauke mutane domin samun kudin fansa.

Wadannan laifuffuka sun ci karo da sashe na 6 na dokar shekarar 2009 da ta haramta yin garkuwa da mutane a jihar Imo.

Haka zalika ana zargin an same su dauke da bindigogin AK-47 har uku da wata ‘yar karamar bindiga da tulin harsashi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

DSS ta yi karar wasu mutane da sun tsere

A gefe guda akwai mutane biyu - Aminu Haliru, 27 da Tange Ibrahim, 20 (Jijji) da ake zargi da laifin sace mutane hudu.

An ce sun yi aika-aikar ne ranar 4 ga Oktoba 2026 a tsakanin garin Owerri zuwa Mgbidi, amma daga baya an ceto matafiyan.

Masu kara sun ce mutanen nan biyu da yanzu ba a san inda suka shige ba, sun karbi N8m kafin su saki wadanda suka kama.

Bayanai sun ce ana zargin su da mallakar AK-47 da wata bindiga kirar gida ba bisa ka’ida ba.

Kudi N1.8m da aka samu a wajen su suna cikin hujjojin da aka gabatar, jami’in DSS kuma yana cikin masu ba kotu shaida.

'Yan sanda
Wani dan sanda a bakin aiki a Lekki, jihar Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'APC ba za ta iya magance rashin tsaro ba'

Abdulaziz Yari ya ce idan tsohon soja irin Muhammadu Buhari bai kawo tsaro ba, me ake tsammani daga Bola Tinubu.

An ji labari jam’iyyar ADC ta soki wannan magana, tana mai cewa gwamnatin APC ta da dabarun kawo zaman lafiya.

Kakakin ADC-PCC, Kola Ologbondiyan yana so Tinubu ya magance matsalar tsaro maimakon neman ƙarin wa’adi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng