'Yan Baranda sun kashe Mutane 6 a jihar Zamfara

'Yan Baranda sun kashe Mutane 6 a jihar Zamfara

Mun samu cewa kimanin rayukan Mutane 6 ne suka salwanta da suka hadar da wani jami'in dan sanda yayin da 'yan Baranda suka kai wani mummunan hari kauyen Gurbin Bore dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, shine ya bayar da tabbacin aukuwar wannan lamari da ya auku a daren ranar Juma'ar da ta gabata.

SP Shehu yayi ganawarsa da manema labarai a jiya Asabar ya bayyana cewa, wannan mummunan hari ya auku ne yayin da 'yan barandan kimanin su 100 suka afka kauyen na Gurbin Bore da misalin karfe 10.00 na daren Juma'a.

'Yan Baranda sun kashe Mutane 6 a jihar Zamfara

'Yan Baranda sun kashe Mutane 6 a jihar Zamfara
Source: Depositphotos

Baya ga salwantar rayukan Mutane 6, akwai kimanin Mutane 3 da suka jikkata sakamakon wannan mummunan hari da a halin yanzu ke samun kyakkyawar kulawa wurin kwararru na kiwon lafiya.

KARANTA KUMA: Mun raina nadin mukamin Kujerar Sakataren Gwamnatin tarayya - Bukatar PDP reshen Kudu Maso Yamma ga Atiku

A yayin ganawarsa da manema labarai mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi, Alhaji Abubakar Dauran, ya bayyana cewa wannan hari ya salwantar da Shaguna 13 da kuma Motoci 15 da 'yan Barandan suka kone.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar Hisbah mai tabbatar da da'a da tarbiyya a tsakankanin al'umma ta cafke wani kasurgumin Kwarto da ya sharaha wajen yin lalata da Matan Aure a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel