An Ji Dalilin Gwamnati Na Soma Karbe Rijiyoyin Mai nan da ‘Yan Kwanaki Masu Zuwa
- Gwamnatin Tarayya za ta fara soke lasisin rijiyoyin da ba a fara hako mai a cikinsu ba daga mako mai zuwa
- Hukumar NUPRC ta ce masu lasisi za su rasa su idan suka kasa fara aiki cikin wa’adin da aka kayyade masu
- Matakin na da nufin hana masu lasisi rike dukiya ba tare da amfani da su ba a cewar Oritsemeyiwa Eyesan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Gwamnatin Tarayya za ta fara soke lasisin wasu rijiyoyin da ba a fara hako mai a cikinsu ba daga mako mai zuwa.
Matakin na zuwa ne domin dawo da kadarorin da masu lasisi suka kasa fara cin moriyarsu a cikin wa’adin da aka kayyade.

Source: Getty Images
Za a soma karbe lasisin rijiyoyin mai
Punch ta ce Shugabar Hukumar NUPRC mai kula da hako mai a Najeriya (NUPRC), Oritsemeyiwa Eyesan ta shaida hakan.

Kara karanta wannan
Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare
Oritsemeyiwa Eyesan wanda aka nada a 2025 ta bayyana hakan a wani taron horas da masu lasisin hako mai da aka yi a Legas.
Za a kwace lasisin wadanda suka kasa fara aikin hako mai cikin wa’adin shekaru uku da ake ba rijiyoyin da ke doron kasa.
Ta ce rijiyoyin mai da ke cikin teku suna da shekaru biyar su fara amfani da shi.
NUPRC ta ba masu rijiyoyin mai zabi 2
Oritsemeyiwa Eyesan ta jaddada cewa gwamnati ba za ta kyale masu rike da lasisi su zauna ba su hako komai a rijiyoyinsu ba.
Ta ce masu lasisin za su fuskanci zabi biyu: su fara hako mai ko su rasa lasisin da aka ba su.
Misis Oritsemeyiwa Eyesan ta ke cewa haka wannan tsari yake a kasar Nederlands, Ingila da duk sauran kasashen duniya.
Shawarar da aka ba masu harkar hako mai
Ta bayyana cewa wasu masu lasisi na samun matsala ne saboda rashin kwararrun ma’aikata, abokan hulda ko kudin aiki.
Sai dai hukumar NUPRC ta kasa ta ce wadannan matsaloli ba su isa su zama dalilin kara masu wa’adin lasisi kai tsaye ba.
Ta kuma shawarci sababbin masu lasisi da su tabbatar suna da kwararru, kudi da ingantaccen tsarin kafin su fara hakar mai.
A haka ne kuma Daily Trust ta rahoto hukumar ta na cewa za ta bada cikakken goyon baya ga masu lasisin PPL a fadin kasar nan.
Hukumar za ta taimaka masu wajen ganin sun hako mai, ba kawai su yi ta zama da rijiyoyin da ba a cin moriyarsu da kyau ba.
Najeriya na harin karin gangunan mai 250, 000
Da ta ke magana ranar Talata, Oritsemeyiwa Eyesan ta ce suna sa ran samun karin akalla gangunan mai 250, 000 duk rana.
Wadannan ganguna za su fito ne daga wajen mutane 22 da aka ba rijiyoyin mai a rabon karshe da gwamnati ta yi a kasar.
Ana sa ran wannan adadi ya dore na tsawon shekaru biyar daga rijiyoyin da aka raba a shekarar 2022/2023 da kuma 2024.

Source: Getty Images
Yadda gwamnati za ta raba rijiyoyin mai
An ji Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za a dogara ga yawan kudi kadai ba wajen raba rijiyoyin mai, sai an duba kwarewa da cancanta.
Daga cikin kamfanoni 286 da suka nemi lasisi, 196 ne suka cancanci shiga mataki na gaba domin neman lasisin rijiyoyin mai 50 da aka bada dama.
An yi hakan ne domin tabbatar da an damka rijiyoyin ga kamfanonin da za su yi amfani da su wajen hako mai ko gas ba tare da sun bar su haka nan ba.
Asali: Legit.ng

