Kano: Bayan Biyo Kwankwaso a Yawan Ƙuri'u a 2023, Nawa Tinubu Zai Samu a 2027

Kano: Bayan Biyo Kwankwaso a Yawan Ƙuri'u a 2023, Nawa Tinubu Zai Samu a 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya samu kuri’u 517,341 a Kano a zaɓen 2023, amma har yanzu ana tambayar ko zai iya lashe jihar a 2027
  • Rabiu Kwankwaso, wanda ya lashe zaɓen 2023, yanzu yana takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a ƙarƙashin jam’iyyar NDC
  • Atiku Abubakar, Peter Obi da Tinubu na fafatawa domin samun goyon bayan masu zaɓe a Kano, yayin da sabon tsarin siyasa ke tasiri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, hankalin mutane da dama, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, ya karkata zuwa Kano.

Kamar yadda aka saba a zaɓukan baya, Shugaba Bola Tinubu na APC, Alhaji Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi na NDC na fafatawa domin samun ƙuri’un Kano.

Hankula sun koma kan zaben shugaban kasa a Kano
Rabi'u Kwankwaso, Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Bayo Onanuga, Peter Obi.
Source: UGC

2023: Wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Kano

Kara karanta wannan

Jam'iyyun adawa 3 Sun haɗa kai da APC domin yallata Shugaba Tinubu, an jero sunayensu

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ne ya lashe zaɓen a jihar Kano, cewar Vanguard.

Kwankwaso ya samu ƙuri’u 997,279, inda ya kayar da Tinubu, wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 517,341.

Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya samu ƙuri’u 131,716. Peter Obi na jam’iyyar LP kuma ya samu ƙuri’u 28,513.

Shekaru huɗu bayan zaɓen 2023, wasu abubuwa sun sauya duk da cewa manyan ’yan takarar suna nan suna fafatawa.

Bambancin takarar Kwankwaso a 2023 da 2027

A yanzu, Kwankwaso ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi, ba shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsu ba.

Shin masu zaɓe a Kano za su ci gaba da ba shi irin goyon bayan da suka ba shi a baya, duk da cewa ba shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa ba?

A gefe guda, shin za su karkata ga Atiku, wanda shi ma ɗan Arewa ne kuma yake takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC?

Ko kuwa masu zaɓe a Kano za su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu, wanda yake takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, domin ya samu ƙuri’u fiye da 517,341 da ya samu shekaru huɗu da suka wuce?

Kara karanta wannan

Abin da ya fi firgita Kashim Shettima kan zaben 2027 fiye da Atiku da Obi

Waɗannan su ne tambayoyin da za a samu amsoshinsu nan da kwanaki 86 da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a fadin Najeriya.

Abba Kabir ya tallata Tinubu a Arewa

A wani labarin, an ji cewa Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da goyon bayan Arewa ga burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce Kano za ta jagoranci sauran jihohin Arewa wajen ƙarfafa fitowar masu kaɗa ƙuri’a ga Tinubu.

Kungiyar Arewa for Asiwaju, ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, na son tallata ayyukan Tinubu da tattara goyon baya ga tikitin Tinubu da Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.