Allahu Akbar: Labarin wani gurgu da ya samu mukami a ofishin Shugaban Majalisa

Allahu Akbar: Labarin wani gurgu da ya samu mukami a ofishin Shugaban Majalisa

Kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila ya nada Abdulsalam Idowu Kamaldeen a matsayin sabon mai bashi shawara na musamman akan bukatu na musamman.

Abdulsalam Idowu Kamaldeen mai shekara 49, ya samu nakasa a lokacin da ya cika shekara uku a duniya sakamakon cutar shan inna.

Abdulsalam ya fara karatun firamare yana da shekara takwas a shekarar 1978 a Erin-Ile, jihar Kwara. A wannan shekarar ne kuma ya fara bara a kan titi saboda rashin kudi. Daga nan sai ya kammala karatun firamare a 1993 sannan ya tai Lagas, inda anan yake bara tare da samun tallai yayinda yake kwana a gargashin gadar Dosunmu.

Bayan kammala karatun sakandare, sai ya fara zuwa darasin yamma. Ya samu gurbin shiga jami’a don karantar kimiyar siyama a UNILAG a 2006 sannan ya kammala karatu a 2010. A kokarinsa na son zama lauya sai ya rubuta jarrabawar JAMB sannan ya samu shiga jami’ar Lagas domin karantar karatun lauya a 2010. Ya kammala a 2015.

Daga nan Abdulsalam ya tafi makarantar lauyoyi na Najeriya, inda ya lashe dukkanin takardunsa a zama na farko sannan ya zama cikakken lauya a 2016.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Ana shirin haramta sana’ar adaidaita sahu a Kano

Kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila a lokacin da yake a matsayin Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, ya gano Abdulsalam Kamaldeen sannan ya gayyace shi zuwa zauren majalisa a 2017 domin majalisa ta yi masa karramawa na musamman.

Kamaldeen ya fito ne daga jihar Kwara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng