Dan Majalisar Dokokin Kano Ya Kira Ruwa bisa Zargin Zagin Gwamna Abba

Dan Majalisar Dokokin Kano Ya Kira Ruwa bisa Zargin Zagin Gwamna Abba

  • An dakatar da Yusuf Bello Aliyu na tsawon watanni uku saboda zargin furta kalaman cin mutunci ga gwamnan Kano
  • Matakin ya biyo bayan wani bidiyo da aka nuna ɗan majalisar yana riƙe da zomo ta kunnuwansa yayin furta kalaman da aka ɗauka a matsayin cin mutunci
  • Majalisar ta bukaci ɗan majalisar ya bayyana a gabanta tare da neman gafarar gwamnan a bainar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wani dan majalisa bisa zargin cin mutuncin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Majalisar ta dakatar da Yusuf Bello Aliyu, ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa, na tsawon watanni uku bisa zargin furta kalaman cin mutunci ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An dakatar da dan majalisa kan zargin zagin Gwamna Abba
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa Majalisar ta ɗauki matakin ne yayin zamanta na ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sake nada kwamishinan da ya bar gwamnati bayan wasu zarge zarge

A yayin zaman, majalisar ta umarci ɗan majalisar da ya nisanci dukkan ayyukan majalisa a tsawon lokacin dakatarwar.

Zaman majalisar ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore.

Bidiyon da ya jawo dakatarwar

Dakatarwar ta biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo da aka nuna Yusuf Bello Aliyu yana riƙe da zomo ta kunnuwansa yayin da yake furta wasu kalamai da aka zarga da cewa cin mutunci ne ga gwamnan.

Kafin ɗaukar matakin dakatarwar, majalisar ta sanar da cewa za ta gayyaci ɗan majalisar domin ya bayyana a gabanta kan bidiyon.

Majalisa ta kafa kwamitin bincike

Hakazalika majalisar ta kuma kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da zarge-zargen da ake yi wa dan majalisar mai wakiltar mazabar Nasarawa.

Bayan kammala aikinsa, kwamitin ya mika rahotonsa ga majalisa, inda daga bisani aka dauki matakin dakatarwa na watanni uku a kansa.

A bisa shawarwarin da kwamitin ya bayar, an umarci Hon. Yusuf Bello Aliyu da ya rubuta wasikar neman afuwa wadda zai karanta a gaban majalisar domin hakan ya zama darasi ga saura.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya hango matsala a dokar zabe da za ta iya shafar sahihancin zaben 2027

An bukaci ya nemi gafarar gwamna

Da yake magana bayan zaman majalisar na ranar Laraba, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce an bukaci Aliyu ya bayyana a gaban majalisar tare da neman gafarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a bainar jama’a.

Sai dai rahoton bai bayyana ko ɗan majalisar ya riga ya amsa wannan buƙata ko kuma ya nemi gafarar gwamnan ba.

Legit Hausa ta tuntubi mai magana da yawun majalisar dokokin jihat Kano, Kamaluddeen Sani Shawai, wanda ya bayyana cewa bai dade da dawowa daga Najeriya.

"Yanzu na shigo Najeriya, tun ina hanya na ke ganin abubuwan da ke faruwa, amma zan nemi bayanai." In ji shi.

Daga baya ya tura bayanan da suke tabbatar da cewa an dakatar da dan majalisar har na tsawon watanni 3.

An dakatar da dan majalisa a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna Abba ya sake nada tsohon kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake naɗa Ibrahim Ali Namadi, tsohon kwamishinan sufuri.

Tsohon kwamishinan dai ya yi murabus ne bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan bayar da belin wani mutum da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng