Wani Direban Mota ya shiga hannu da laifin lalata da Yarinya 'yar shekara 2 a jihar Legas

Wani Direban Mota ya shiga hannu da laifin lalata da Yarinya 'yar shekara 2 a jihar Legas

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Legas, ta samu nasarar cikwikwiye wani Direban Mota da laifin aikata lalata da wata yarinya 'yar shekara biyu da yake makotaka da Mahaiifiyar ta.

Sola Ewulo, dan shekara 38 kuma mazaunin unguwar Agbado dake jihar Legas a Kudancin Najeriya, ya shiga hannu jami'an tsaro a makon da ya gabata yayin da Mahaifiyar wannan Yarinya ta shigar da korafin digar ruwan Maniyyi daga farjin diyar ta.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Imohimi Edgal, shine ya bayar da shaidar wannan mummunan lamari da cewar tuni Sola ya shiga hannu yayin da Mahaifiyar wannan yarinya ta yi korafin Makwabcinta da wannan mugun aika-aika.

Wani Direban Mota ya shiga hannu da laifin lalata da Yarinya 'yar shekara 2 a jihar Legas

Wani Direban Mota ya shiga hannu da laifin lalata da Yarinya 'yar shekara 2 a jihar Legas
Source: UGC

Lamarin ya auku ne yayin da Mahaifiyar wannan Yarinya ta danka kulawar diyar ta a hannun Sola inda ta bazama kan hanyarta ta kasuwa domin cefanen kayan Masarufi.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan dawowarta ke da wuya ta lura da diyarta na fama da sosashe-sosashen da koken radadi a Gabanta inda bayan matsanta bincike ta bayyana sunan Sola a matsayin umul aba isin wannan lamari da take fama da shi.

KARANTA KUMA: Sanata Bukar Abba ya debo ruwan dafa kansa kan furucin rashin nasarar Buhari a Arewa maso Gabas

Imohimi ya bayyana cewa, hukumar 'yan sanda za ta gudanar da binciken diddigi domin gurfanar da Sola a gaban Kuliya inda zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta gano makarkashiyar gami da tuggun da APC da kuma fadar shugaban kasa ke kullawa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel