Annoba Mai Alaka da Kudaje Ta Barke a Gombe, an Samu Asarar Rayuka

Annoba Mai Alaka da Kudaje Ta Barke a Gombe, an Samu Asarar Rayuka

  • Mutane biyu sun mutu bayan barkewar cutar kwalara a ƙauyen Kedo, ƙaramar hukumar Billiri, a ranar 4 ga Oktoba
  • Hakazalika, wasu mutum 74 sun kamu inda aka yi masu magani aka sallame su a asibiti bayan an same su da ita
  • Gwamnatin jihar ta ce za ta ayyana ƙarshen barkewar cutar idan ba a samu sabon kamu ba zuwa ranar 24 ga Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Gwamnatin Jihar Gombe ta ayyana barkewar cutar kwalara a ƙauyen Kedo, da ke gundumar Todi a ƙaramar hukumar Billiri.

Gwamnatin ta ayyana barkewar cutar ne bayan rahotannin gudawa da amai da suka yi sanadin mutuwar mutane biyu a ranar 4 ga Oktoban 2026.

Kwalara ta barke a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Adamu-Danladi Bojude, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Gombe ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Mutane sun bar kasuwancinsu da noma baki daya domin alhinin tsohon gwamna

Ya ce an yi wa mutum 74 da suka kamu da cutar magani kuma an sallame su, yayin da babu wani mara lafiya da ke kwance a asibiti a lokacin taron

An tura tawagar gaggawa domin shawo kan cutar

Bojude ya ce gwamnatin jihar ta gaggauta tura tawagar ba da agajin gaggawa domin taimaka wa jami’an lafiya na ƙaramar hukumar wajen binciken barkewar cutar da kuma ba wa mazauna yankin da abin ya shafa magani kyauta.

Ya ce ana ba da wannan magani ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Firamare da ke Sheila.

“Tun daga lokacin, an yi wa mutane 74 magani aka sallame su, kuma babu wanda ke kwance a asibiti a halin yanzu.”

An shafe kwanaki 7 ba tare da sabon kamu ba

Kwamishinan ya ce zuwa ranar 21 ga Oktoba, an shafe kwanaki bakwai a jere ba tare da samun rahoton sabon kamuwa da cutar ba.

Ya bayyana fatan cewa za a ayyana ƙarshen barkewar cutar idan ba a samu wani sabon kamu ba zuwa ranar 24 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin da ya ritsa da jariri da wasu mutane a Kaduna

“Yau, 21 ga Oktoba, ita ce rana ta bakwai da ba a samu rahoton sabon kamu ba. Idan aka kai rana ta goma, wato 24 ga Oktoba, ba tare da an samu sabon kamu ba, za a ayyana cewa wannan barkewar cutar ta ƙare.” In ji shi.

Gwamnati ta ƙarfafa matakan rigakafin kwalara

Bojude ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, gwamnatin jihar ta ƙarfafa matakan rigakafin cutar kwalara ta hanyar shirin rigakafi da ake aiwatarwa duk shekara.

Ya ce Ma’aikatar Lafiya ta jihar ce ke aiwatar da shirin tare da haɗin gwiwar Hukumar Samar da Ruwan Sha da Tsaftar Muhalli ta Ƙauyuka (RUWASSA) da sauran abokan hulɗa.

A cewarsa, shirin ya shafi wurare sama da 150 da aka gano a matsayin wuraren da cutar kwalara ta fi samun damar barkewa, a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar. Ya ce shirin ya taimaka matuƙa wajen rage yawan barkewar cutar a jihar.

Kwalara ta barke a Gombe
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Twitter

Cutar Ebola ta shigo Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar Ebola guda ɗaya a babban birnin tarayya, Abuja.

Majiyoyi sun bayyana cewa an fara binciken waɗanda suka yi hulɗa da majinyaciyar saboda dakile yaduwarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng