Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya tayi zarra a tsakanin daliban ABU

Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya tayi zarra a tsakanin daliban ABU

An samu wata daliba mace daga jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zariya da ta ciri tuta a tsakanin kafatanin daliban jami’ar gaba daya ta hanyar lashe lambar yabo ta dalibar da tafi hazaka a jami’ar gabaki daya.

Wannan daliba sunanta A’eesha Abdullahi Abaji, yar asalin jahar Nassarawa, amma mazauna garin Jos na jahar Filato, kamar yadda ta shaida ma majiyar Legit.ng a wata tattaunawa da tayi da ita.

Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya da tayi zarra a tsakanin daliban ABU

A'eesha
Source: UGC

KU KARANTA: Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS guda 9

Ita dai A’eesha ta karanci ilimin likitanci ne a ABU, sai dai kafin nan ta bayyana ma majiyarmu cewa ta yi makarantar Firamari a Plateau Private School, Jos, da sakandari a Airforce Girl’s Comprehensive School, Jos.

Kallabi tsakanin rawwuna: Yadda wata Ustaziya da tayi zarra a tsakanin daliban ABU

A'eesha
Source: UGC

Ta kara da cewa tafi son darussan lissafi watau Maths, dana ilimin halittu, Biology, hakan ne ma yasa ta kudurci karantar ilimin likitanci a jami’a, duk da cewa dai tana da karancin shekaru, musamman ma a ajisnu a ABU, amma duk da haka ta dage, sai gashi ta zamo zakarar gwajin dafi.

Daga cikin kyautukan da A’eesha ta lashe a matsayinta na dalibar likitanci akwai ‘Community Medicine, Haematology, Internal Medicine, Medical microbiology, Obstetrics & Gynaecology, Pharmacology, gwarzon Mace a darasin Pharmacology, da kuma kyautar gwarzuwar gwaraza ta NMA.

Daga karshe Ustaziya A’eesha ta gode ma Allah da wannan nasara data samu, kuma tayi fatan Allah Ya cika mata burinta na samun miji nagari ta yi aure, ta zama uwa, sa’annan kuma ta cigaba da karatu domin ta kware a bangaren likitancin kananan Yara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel